Monday, February 4, 2019

[LABARAI] A RANAR DA ZAN FARA SHIGA ZAN TSAIDA YAJIN AIKIN MALAMAN JAMI'O'I - ATIKU





Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin
jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha
alwashin cewa idan aka zabe shi, to zai
kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in
kasar a ranar da ya fara aiki.

Ya yi wannan alwashin ne a taron bayar da
lambobin yabo na Gwarzon Shekara da
Silver Bird ya shirya a Legas.

Ya ce farkon abin da zai fara yi a ranar da
aka rantsar da shi, shi ne nada ministocin
sa, kuma a wannan ranar ce zai magance
matsalolin yajin aikin lamaman jami’a.

Atiku ya ce ilmi a kasar nan ya yi tsaye cak
wuri daya, tun bayan da aka fara yajin aiki,
watanni hudu da suka gabata.

“Abin kunya ne a ce daliban jami’a na gida
zaune na su karatu, har tsawon watanni
hudu, an kasa shawo kan matsalar.”

Wazirin Adamawa ya ce idan aka zabe shi,
ya yi alkawarin nunka kudaden da
gwamnatin tarayya ke kashewa a fannin
ilmi har zuwa nunki uku.

“A yanzu gwamnati na kashe kashi 7 bisa
100 na kasafin kudi a fannin ilmi. Amma ni
idan aka zabe ni, to zan rika ware kashi 20
visa 100 na kasafin kudi ga fannin ilmi.” Inji
Atiku.

No comments:

Post a Comment