Monday, January 28, 2019

[LABARAI] INA TARE DA HUKUNCHIN DA AKA YANKE NA BABU DAN TAKARA A.P.C A JAHAR ZAMFARA - SANATA MARAFA
Sanatan dake wakiltar jihar Zamfara a
majalisar dattawa Kabiru Marafa ya yaba
wa hukuncin da kotu ta yanke na kin
amincewa da dan takara koda daya ne na
jam’iyyar APC daga jihar.

Idan ba a manta ba hukumar Zabe ta sanar
cewa ba za ata amince da dantakara ko daya
ba daga jam’iyyar APC a jihar zamfara cewa
jam’iyyar ta kasa gudanar da zaben fidda
gwani har lokacin da aka dibar mata ya
wuce.

A jerin sunayen da hukumar ta fitar babu
dan takara ko da daya ne daga jihar
Zamfara da ta saka.

Sanata Marafa ya ce abinda hukumar ta yi
da hukuncin kotu shine ya fi dacewa da
jam’iyyar APC a jihar.

Sai dai kuma ana haka ne Kotu a garin
Gusau ta yanke hukuncin cewa a saka
sunayen ‘yan takara na jam’iyyar APC a
cikin jerin wadanda za su fafata a zabe mai
zuwa.

Gwamnan jihar AbdulAziz Yari ya yaba wa
wannan hukunci da kotun jihar ta yanke sai
dai kuma sanata Marafa ya ce ba zai amince
da wannan hukunci da aka yanke ba.

Marafa ya ce ko da ko karfin sa zai kare ne
zai tabbata hakan bai tabbata ba domin idan
ma aka nemi amfani da wannan hukunci na
kotun Zamfara zai garzaya kotun daukaka
kara.

No comments:

Post a Comment