Jam’iyyar APC mai mulki ta zargi hukumar Zabe da yi wa jam’iyyar PDP aiki don ganin ta kada jam’iyyar a zabuka masu zuwa.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole ya yi wannan korafi da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Oshiomhole ya zayyano dalilan sa kamar haka:

1 – Har yanzu akwai wasu kwamishinonin hukumar Zabe da ke aiki a yankin Kudu Maso Kudu wanda dukkan su ‘yan PDP ne.

2 – Kin amincewa da ‘yan takarar jam’iyyar APC na jihar Zamfara da hukumar taki yi shima duk nuni ne na yi wa jam’iyyar PDP sai ti domin ta kada mu.

Bayan haka Oshiomhole ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta yiwo hayan sojojin haure ne inda suka cika Fam Kano. Ya ce kowa ya sani cewa hayan mutane suka yi a Kano.

Oshiomhole kuma ya yi amfani da wannan dama ya maida wa jam’iyyar PDP martani game da cewa da tayi wai ‘yan APC ne suka kona ofisoshin hukumar Zabe domin sun sani cewa tasu ta kare.

 Oshiomhole ya ce wannan zance kanzon kurege ne domin sune ma suke zargi da kone ofisoshin domin sun ga cewa ba za su yi nasara a zabe ba.

” Ina so in sanar wa PDP cewa su kwana da shirin kwashe kashin su a hannu ranar Asabar domin watsa-watsa da su jam’iyyar APC zata tayi. Abin da suke fadi da yi a yanzu duk burin kunya ne.