Thursday, February 21, 2019

[LABARAI] INEC TA BAYYANA KO NAWA ZATA BA MA'AIKATAN ZABE





ZABE: Naira 30,500 za a biya
ma’aikatan wucin-gadi – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa,
INEC ta ce za ta biya kudin ladar aikin zabe
naira 30,500 ga dukkan masu bautar kasa
(NYSC) da suka shiga aikin zabe.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood
Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Laraba
a lokacin da ya ke wa manema labarai
jawabi dangane da sabbin shirye-shiryen da
aka samu wajen gudanar da zabe a ranar
Asabar mai zuwa.

Yakubu ya ce za a biya kowane dan NYSC
alawus na ladar aikin sa, naira 30,500.
Wannan bayani ya zo ne kwana daya bayan
da wasu masu bautar kasa da za su yi akin
zabe suka rika watsa labarin cewa an fara
biyan kudin alawus na INEC, amma akwai
bambancin yadda aka biya wasu ya sha
bamban da abin da aka biya wasu.

An ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta
gabata, da dama daga cikin su sun kai kan
su wuraren da za su yi aiki ne bayan da
INEC ta yi jinkirin biyan su kudaden alawus
na tirenin har naira 4,500 da aka yi musu
alkawari.

Wannan ya sa masu bautar kasa suka rika
yada barazanar cewa idan ba a biya su
kudaden ba, to ba a su yi aikin zaben ba.
Sun rika watsa wannan bayani a wani
zauren su na WhatsApp.

Wannan ya sa nan da nan aka fara biyan su,
kuma suka yi sanarwar cewa an fara biyan
su alawus na tirenin din, watau naira
4,500.00 Sai dai kuma ya zuwa jiya Laraba, wasu
jihohin ne suka fara samun ‘alert’, wasu
kuma ba su kai ga samu ba.

INEC dai gaba daya za ta biya ladar zuwa
horaswar sanin makamar aiki ta naira
4,500. Kenan a zaben shugaban kasa da
majalisar dattawa da ta tarayya, za su karbi
naira 17,500.

Sai kuma sai zaben gwamna da na majalisar
jiha, za a biya su naira 13,000. Gaba daya
kudin sun kama naira 30,500 kenan.
Yakubu ya ce an tanadar wa kowane dan
bautar kasar da zai yi aikin INEC kayan
katifun kwanciya da mayafi da kayan wanka
da bandakuna da kuma wutar lantarki da
jami’an tsaro a cibiyoyin zaben da aka tura
kowanen su.

Ya ce duk an tanadar musu da wadanan
idan su ka isa wuraren a jajibirin ranar
zabe, duk za a raba musu kayayyakin.

No comments:

Post a Comment