Thursday, February 21, 2019

[LABARAI] BAZANYI MARABUS DAGA HUKUMAR ZABE BA - MAHMOOD YAKUBU
Ba zan yi murabus ba daga
shugabancin Hukumar Zabe –
Mahmood Yakubu

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mahmood
Yakubu ya bayyana cewa ba zai you
murabus ba kamar yadda wasu ke Kira da
yayi.

Mahmood ya ce idan da ko akwai dalilin yin
murabus din ko tantama ba zai yi ba, zai
mika takardar sa ya Kara gaba.
” Bana cikin takura ko matsi a hukumar da
zai sa in ajiye aiki na. Amma fa idan da
akwai dalili, ko tantama ba zan yi ba, zan
karkade takalma na in ajiye musu aikin su
in Kara gaba. Akwai aikin da hukumar na
tabbatar da ayi Zabe Kuma shine a gaba mu
yanzu.

Sai dai Kuma shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya bayyana cewa da zarar an
Kammala zabukan dake gaba, zai bi diddigin
musabbabin dage Zabe da aka yi a
Kwanakin baya.

Wannan furuci da yayi ya kawo cecekuce a
kasa Inda wasu ke ganin shugaba Buhari ya
riga ya ya san da cewa shine zai lashe zaben
dake tafe.

No comments:

Post a Comment