Tuesday, June 26, 2018

[LABARAI] YADDA AKA KASHE MUTUM 86 A JIHAR FILATO 25 YUNI 2018




Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da
'yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka
kashe biyar daga cikinsu.

Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya ya kai ga
kisan wasu karin mutanen.

Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima
kan mallakar filaye.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan
ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Tun da farko an kashe gwamman mutane a wani rikici mai kama da
wannan tsakanin Fulani da mafarauta a kasar Mali.

Tuni dai aka kafa dokar hana fita a wasu yankuna uku na jihar ta
Filato.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Undie Adie ya ce binciken da aka
gudanar a wasu kauyuka bayan kai harin ya tattabatar da cewa an
kashe mutum 86, sannan wasu shida su ka samu rauni.

Ya ce an kona gidaje 50, da baburan hawa 15 da kuma motoci biyu.

Kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Datti ya shaida wa BBC
cewa dokar hana fitar za ta yi aiki daga karfe shida na yamma zuwa
shida na safe a Riyom, da Barikin Ladi da kuma Jos ta Kudu "domin
hana jama'a daukar doka a hannunsu da samar da zaman lafiya".

Sai dai sabanin bayanin 'yan sanda, Mr Datti ya ce sama da mutum
20 ne suka jikkata, kuma suna samun magani a asibitoci daban daban.

Tare hanya

Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare
hanya su na kashe mutanen da 'ba su ji ba, ba su gani ba,' wadanda
yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas
kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.

Su wayeFulani Makiyaya?

1- Suna daga cikin ƙungiyar makiyaya mafi girma a duniya kuma
ana samun su a yammaci da kuma yankin tsakiyar Afrika, daga
Senegal zuwa jamhuriyar Tsakiyar Afrika

2- A Najeriya wasu sun cigaba da zama a matsayinsu na makiyaya,
yayin da wasu suka koma birane

3- Fulani makiyaya suna yin akasarin rayuwarsu a daji ne, ba kamar
mutanen da ke zama a cikin birane ba, kuma suna da alaƙa da
waɗannan rikice-rikicen

4- Suna kiwon dabbobinsu a yankuna da dama, inda suke yawan yin
rikici da al'ummomin da galibin aikinsu noma ne

5- Ana yawan dangantasu da ƙabilar Hausa, saboda tsawon lokacin da
suka shafe suna zama tare

6- Fulani sun taka muhimmiyar rawa a ƙarni na 19 wajen farfaɗo da
addinin Musulunci a Najeriya.

Me ke kawo rikicin?

Ana tunanin ce-ce-ku-ce a kan abubuwan more rayuwa kamar su
gonaki da yankunan da ke da burtali da ruwa ne ke jawo rikici
tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Fulani makiyaya kan iya tafiya mai nisa tare da dabbobinsu domin
nema musu abinci. Mafi yawan lokuta, suna daukar makamai domin
kare dabbobin nasu.

Suna yawan rikici da manoma wadanda ke yawan cewa suna lalata
musu amfanin gona kuma ba sa kula da inda dabbobin nasu ke zuwa.

Fulanin na zargin cewa manoma waɗanda ke ƙoƙarin satar shanunsu -
suna cewa suna ƙoƙarin kare kansu ne.

A da, rikicin a yankin tsakiyar Najeriya aka fi yi, inda kiristoci
ƙabilar Birom da ke jihar Plateau suke kisan ramuwar gayya ga
Musulmai da makiyaya.

Yadda sauyin yanayi ya ke shafar burtali ya sa Fulani makiyaya sun
kara matsawa zuwa kudancin Najeriya domin neman ruwa da ciyawa.

Wannan ya ƙara faɗaɗa rikicin ta inda ake cigaba da fuskantar
munanan tashe-tashen hankula a kudancin ƙasar, ana ƙara jin tsoron
cewar rikicin zai yi barazana ga haɗin kan da dama ya ke tangal-
tangal tsakanin ƙabilun Najeriya.

No comments:

Post a Comment