Tuesday, June 26, 2018

[LABARAI] SUNAYEN MINISTOCI DA MUKARRABAN BUHARI DA SUKA KARKATAR DA GURABEN KARASunayen Ministoci Da Mukarraban Buhari Da Suka Karkatar Da
Guraben Ka Suka Karkatar Da
Guraben Kara
guraben karo ilmin da CCECC ya ware wa ‘yan Najeriya ga
makusantan su
Daga Premium Times Hausa

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo
muku wani labarin abin kunya, wanda wasu ministoci da manyan
jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari suka handame
guraban da kamfanin gina titin jiragen kasa na kasar China, CCECC
ya ware, domin matasan Najeriya su samu damar zuwa China yin
karatu.

A yau kuma mun bankado muku sunayen ministocin da manyan
jami’an Gwamnati, wadanda su ne suka rabe gurabun karo karatun ga
‘ya’yan su, ‘ya’yan dangin su, na abokan su da kuma kannen matan
su.

1 – Karamin Ministan Harkokin Ilmi, Anthony Onwuka;

2 – Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung;

3 – Karamin Ministan Harkokin Lantarki, Suleiman Hassan;

4 – Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar;

5 – Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi;

6 – Ministan Gona, Audu Ogbe;

7 – Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa,Ade
Ipaye;

8 – Karamin Ministan Harkokin Jiragen Sama, Hadi Sirika;

9 – Karamar Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Aisha Abubakar;

10 – Ministan Harkokin Yankin Neja-Delta, Usani Usani;

11 – Ministan Fasahar Sadarwa, Adebayo Shittu;

12 – Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Udo Udoma.

Duk yawancin wadanda PREMIUM TIMES ta tuntube su domin su
kare kan su, ko kuma ta tuntubi kakakin yada labaran su, sun kasa
cewa komai.

Wasu kuma idan an kira ba su dauka, ko an yi musu sakon tes, ba su
maido amsa. Duk sun yi shiru, wai malam ya ci shirwa.

Source Premium Times

No comments:

Post a Comment