Sunday, January 20, 2019

[LABARAI] JERIAN SUNAYEN GWAMNONI 15 DA BASU GOYON BAYAN KARIN ALBASHI A NIGERIA





Gwamnoni 15 da ba su goyon bayan karin albashi

Shugaba Muhammadu Buhari bai ware kowace jam’iyya ba, a lokacin da ya ce kada zabi duk gwamnan da bai tabuka abin kirki ba, musamman kasa biyan albashi.

A lokacin da ya ke magana da Shashen Hausa na Muryar Amurka, ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnoni su kasa biyan albashi ba, duk kuwa da bimbin kudaden da ya gabza musu.

‘Na rasa yadda gwamna zai iya barci, alhali ya na sane da cewa bai biya albashi ba.. ma’aikatan nan akwai matsaloli a gaban su. Ga kudin haya, ga kudin makarantar yaran su ga kuma kudin kulada lafiyar su.” Inji Buhari.

PREMIUM TIMES ta yi amfani da wasu bayanai sahihai daga rumbun bincike na BudgIT, wata kungiyar sa-kai da sa-ido, inda aka tattara jihohin da ma’aikata ke bin dimbin bashin albashi da ba biya su ba.

A cikin Oktoba, 2018, BudgIT ta buga sunayen gwamnonin da ma’aitakan jihar sa ke bin bashin kudaden alawus da albashi duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi kudin ceto su daga halin kaka-ni-ka-yi har naira tiriliyan 1.8.

1 – ABIA: Ya zuwa watan Oktoba, 2018, malaman sakandare na bin bashin albashi na wata biyar, kuma an kai watanni 18 ba a biya kudaden ‘yan fansho ba. a farkon hawan sa cikin 2015, an yi ta murna ganin yadda ya biyar tsohon bashin kudaden albashi na watanni takwas. Amma shi kuma a yanzu ya kasa biya. Ya sake tsayawa takarar gwamna a karo na biyu.

2 – ADAMAWA: Gwamnan Adamawa daga Oktoba, an gano ya kasa biyan ma’aikatan sakatariyar gwamnatin jihar albashin watanni hudu, watanni hudu bai biya ma’aikatan jiyya albashi ba, sannan kuma malaman sakandire wata biyu, su kuma ‘yan fansho har tsawon watanni 13 rabon su da na su hakkin.

Gwamna Bindow ya kuma kasa biyan ma’aikatan kananan hukumomi albashi. Cikin Nuwamba ya nemi amincewar majalisar jiha domin ya ciwo bashin naira bilyan biyar daga bankuna, domin yarage albashi. Shi ma ya fito takarar sake hawa kujerar gwamna.

3 – AKWA-IBOM: Gwamna Emmanuel Udom, ya gaji dimbin bashi daga hannun wanda ya gaji gwamnati a hannun sa, Godswill Akpabio. Ya yi kokari ya biya har zuwa na karshen shekarar 2015. Amma sai a cikin 2018 ya kammala biyan albashi da alawus na gwamnatin da ya gada tun 2015.

BudgIT, a cikin Oktoba ta gano cewa tsoffin ma’aikatan jihar na bin bashin kudin fansho na wata sha biyu. Rabon da a biya kudin fansho tun cikin 2016.

Amma dai ma’aikata ba su bin bashin albashi ko na naira daya.

4 – BAYELSA: Jihar Bayelsa ta na biyan albashi da fansho, amma dai akwai tsoffin kudaden ariyas na albashin wata uku da rabi tun na 2016, da har yau ba a biya ma’aikata ba.

Shi ma ya sake fitowa takarar gwamna, ya na neman zarcewa.

5 – BENUWAI – Ma’aikatan da ke daga matakin albashi na 8 zuwa na 10, sun a bin albashi na daga watanni hudu, har ma akwaimasu bin na wattanni 11. Ortom ya ce ya gaji bashin naira bilyan 67 da gwamnatin da ya gada ta kasa biyan albashin ma’aikata da su. Ya kuma gaji wani bashin na naira bilyan 70 na garatuti da sauran kananan basussuka.

6 – BARNO – BudgIT ta binciko cewa ana bin gwamnan jihar kudin ariyas na watanni biyu kacal, kuma shi ma kokarin tantancewa da ake yi ne ya kawo jinkiri.

7 – DELTA – Masu karbar fansho na bin gwamnatin jihar bashin makudan kudaden da aka dade ba a biya su ba. an hakkake ‘yan fansho na bin bashin watanni 36, kuma har zuwa lokacin da kae hada wannan labari, babu tabbacin cewa an fara biya.

8 – IMO – Cikin 2016, Gwamnatin Jihar Imo ta cimma yarjejeniyar biyar kashi 70 cikin 100 na ma’aikatan jihar. Amma su wadanda ke daga mataki na 0-06, aka rika biyan su kashi 100 bisa dari.

Ma’aikata na bin albashin watanni biyu, su kuma kudaden ‘ayn fansho wata 36 ba a biya ba.

Okorocha ya fito takarar sanata karkashin APC.


9 – KOGI: Gwaman Kogi, Yahaya Bello, ya na biyan ma’akatan sakatariyar gwamnati kashi 50 bisa 100, su kuma ma’aikatan jiyya kashi 40 bisa 100. Duk da haka, ana bin sa albashi da fansho daga masu watanni biyu sai masu watanni 13.Shi ma ya sake fitowa takara.

10 – KWARA: Malaman sakandare na bin Jihar Kwara albashin wattani hudu, sai dai kuma gwamna Abdulfatah Ahmed zai kammala wa’adin sa na shekaru takwas.

11 – ONDO: Cikin watan Nuwamba da ya gabata ne Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Ondo, Tayo Ogunleye, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya kudaden ariyas na albashin wata shida daga cikin watanni bakawi da ma’aikata ke bin bashi. Ta kuma yi alkawarin biyan sauran cikon wata daya da ya rage a karshen watan Janairu da muke ciki.

Rotimi Akeredulu gwamnan jihar ba zai sake shiga zabe ba, sai cikin 2010.

12 – OSUN: Yayin da gwamnatin jihar ta samu har naira bilyan 16.6 daga cikin kudaden Paris Club, sai gwamnan jihar ya yi sanarwar biyan ma’aikata albashinn su da kudin sallama da na fansho na tsawon wata hudu.

Sai dai kuma abin da ka biya su kawai cikin cokali ne, domin wasu na bin gwamnati bashin kudade har na tsawon watanni 30 da aka shafe ana biyan su kashi 50 cikin 100 kacal.

13 – FILATO: An biciko tsoffin ma’aikata na bin jihar bashin kudaden fansho na tsawon watanni 16. Gwamnan jihar Simon Lalong na kokarin yin tazarce.

14 – TARABA: Ma’aikatan ungowarzoma na bin bashin kudin ariyas na wata daya, su kuma ‘yan fansho na bin na wata biyu ya zuwa cikin watan Oktoba, 2018. Darius Ishaku gwamnan jihar ba zai shiga zabe a wannan shekarar ba, sai 2010 zai cika shekara hudu a kan mulki, sannan INEC ta shirya wani zabe. Tunda shi da na Ondo duk cikin 2016 aka zabe su.

15 – ZAMFARA: Ya zuwa cikin watan Octoba, 2018, malaman sakandaren jihar kudaden ariyas na watanni hudu, su kuma ‘yan fanshon jihar na watanni biyu. INEC ta hana gwamna Abdulaziz Yari ya kammala wa’adin san a shekaru takwas, kuma INEC ta haramta masa tsayawa takarar sanata da ya fito.

No comments:

Post a Comment