Shehu Sani, ya bayyana gwamnan jihar
Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin wanda
bai tsinanawa jihar Kaduna komai ba,
tsawon kusan shekaru 4 na mulkinsa
Sani, ya yi ikirarin cewa, duk da El-Rufai
na da hannu a wajen hanashi tikitin
takara a APC, hakan ba zai canja komai a
siyasarsa ba
Haka zalika, Sanatan ya ya ce akwai
ranar da El-Rufai zai bar ofishin nasa, zai
kuma yi bayani dalla dalla yadda ya
gudanar da mulkin nasa
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta
tsakiya a majalisar dattijai, Shehu Sani, ya
bayyana gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-
Rufai a matsayin wanda bai sanu a ko ina
ba. Haka zalika, Sani, wanda ke takarar
tazarcensa karkashin jam'iyyar PRP, ya ce
babu tsiyar da gwamnan ya tsinanawa
jihar.
Sanata Shehu Sani, ya sauya sheka daga
jam'iyyar APC zuwa PRP, kwanaki uku
bayan da APC ta hana shi tikitin takara a
jam'iyyar. Ya kuma zargi gwamnan jihar
da kulla tuggun da ya sa jam'iyya mai
mulkin ta hana shi tikitin takarar.
Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na
Arise TV a ranar Alhamis, Sani ya ce
jam'iyyar PRP na ci gaba da zama
barazana ga APC a jihar Kaduna, yana
mai cewa, " wannan ne ma dalilin da ya
sa a kowacce safiya da maraice, suna
lalata fastoci da alluran yan takarar
jam'iyyarmu. Suna cutar da
mambobinmu. Idan da a ce mu ba
barazana bane a garesu, da basu kula mu
ba."
Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki
da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna
Sani, ya yi ikirarin cewa, duk da El-
Rufai na da hannu a wajen hanashi tikitin
takara a APC, hakan ba zai canja komai a
siyasarsa ba, inda ya kuma ce "shugaban
kasa Buhari ya ziyarci Kaduna ba sau
daya ba, amma ka taba jin ance yazo
kaddamar da wani aikin da gwamnatin
jihar tayi?"
Dan majalisar dattijan, ya bayyana cewa
shi da El-Rufai ba sa ga maciji, saboda
banbance banbancen da ke tsakaninsu na
siyasa da kuma hangen nesa.
Na shafe kusan gaba daya rayuwata ina
kwatarwa jama'a 'yancin su. A lokacin
mulkin soji, kusan shekaruna sun kare ne
a gidan kurkuku. Ko daga nan zaka
fahimci inda banbancin yake, amma shi
me zainyi takama da shi.?
Ai akwai ranar kin dillanci, akwai ranar
da zai bar ofishin nasa, zai kuma yi
bayani dalla dalla yadda ya gudanar da
mulkin nasa," a cewar Sani.
No comments:
Post a Comment