CIKAKKIYAR TAMBAYAR TARE DA AMSAR DA SHUGABA
BUHARI YA BAYAR.
Karshen tika tika.........
A karon farko Shugaba Muhammad Buhari yayi wa 'yan jarida
bayani game da rikicin zaben fidda gwani na jam'iyar APC na
Jahar Zamfara dama sauran jahohin dake fama da irin wannan
rikici..
Shugaban kasar ya tattauna da Jaridar Thisday ne sakamakon
kin amincewarsa da yayi na shiga cikin presidential debate da
aka shirya na masu takarar kujerar shugabancin kasar.
Sakamakon haka Shugaba Muhammad Buhari ya aminta da
Jaridar Thisday ta tattauna da shi, inda suka gabatar da jerin
tambayoyi masu dama ga shugaban Nijeriyar inda wannan
tattaunawa tasu takai kimanin tsawon mintuna 90. Wadda
wannan tattaunawa ita zata maye gurbin shigarsa a presidential debate da aka shirya.
Acikin jerin tambayoyin, sun gabatar da tambaya ga shugaban
kasa game da rikitattan zaben fidda gwani da jam'iyar APC ta
fuskanta a jahohi da dama. Inda shugaban yayi tsokaci kamar
haka:
Akwai ban mamaki gwamna ya ce wai shi zai fitar da wanda
yake son ya zama gwamna, senata ko dan majalisa. Jam'iyar
APC bata aminta da wannan tsari ba, hasalima hanyoyi guda
uku ne kadai aka amince dasu a wajen fitar da dan takara. Ko
dai 'yar tinke ko sasanci ko kuma zabe ta hanyar delegates. Ya
kara da cewa talakawa su yafi dacewa su fito su yaki duk irin
gwamnan dake kokarin yin wannan ta'asa. Ta hanyar jajircewa
wurin zaben muradinsu. Da kuma kauracewa gwamnonin da
suka yi watanda da kadaden jahohinsu.
Shugaban ya kara da cewa duk da cewa bai so ya shedawa
'yan jarida ba, amma ya zuwa yanzu ya kammala tattaunawa
da jami'an tsaro, cewa ko a lokacin gudanar da zabe (idan
yazo) duk gwamnan da ya nemi yayi magudi domin 'dan
takarar da yake kokarin kakabawa mutane, Shugaban kasa
muhammad Buhari ya dauki alkawarin sai yayi maganinsa.
No comments:
Post a Comment