Friday, January 11, 2019

[SIYASA] BUHARI BAZAI MUSULUNTAR DA NIGERIA BA APC BA JAM'IYYAR MUSULMAI BACHE - OSINBAJO


Buhari ba zai Musuluntar da Nigeria ba,
APC ba jam'iyyar Musulmai ba ce - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da wata manufa na Musuluntar da Nigeria

- Haka zalika, Osinbajo ya ce jam'iyyar APC ba jam'iyyar Musulmai ba ce kadai

- Farfesa Yemi Osinbaj ya ce zaben APC daga sama har kasa, shine zai taimaka wajen kai kasar zuwa mataki na gaba

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da wata manufa na Musuluntar da Nigeria, kamar yadda a hannu daya kuma ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba jam'iyyar

Musulmai ba ce kadai, ba kamar yadda jam'iyyar adawa ke ikirari ba da nufin cusa rikicin siyasar addini a cikin jam'iyyar.

Mataimakin shugaban kasar wanda yake cikin tawagar sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, a jerin manyan kusoshin gwamnatin dasuka samu damar halartar bukin kaddamar ya yakin zaben dan takarar gwamnan
jihar Gombe karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da ya gudana a garin Kaltungo a ranar Alhamis.

Yemi Osinbajo da Boss Mustapha sun yi amfani da taron wajen sanar da daukacin wadanda suka halarci taron a babban filin wasanni na Olusegun Obasanjo da ke Kaltingo, cewar APC ba

wai jam'iyyar Musulumai kadai bace ba, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da wata aniya na Musuluntar da kasar.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya
shaidawa mahalarta taron cewa APC jam'iyyar kowa ce, don haka, kar su yarda jam'iyyar adawa ta rudar dasu da batun addini a cikin siyasarsu, inda kuma ya bayyana cewa kasancewarsa Kirista kuma malamin coci, ya yi aiki da shugaban kasa 
Buhar, kuma ya fahimci cewa shugaban kasar adali ne kuma mai gaskiya.

A yayin da yake kira ga daukacin al'ummar jihar Gombe, da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kad'a kuri'arsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar, Farfesa Yemi Osinbaj ya ce zaben APC daga sama har kasa, shine zai
taimaka wajen kai kasar zuwa mataki na gaba.

A nasa bangaren, sakataren gwamnatin tarayyar, Boss Mustapha ya ce idan da har APC jam'iyyar Musulmai ce kadai, to kuwa da yanzu baya cikin gwamnatin balle har ya rike wannan muhimmin mukami na sakataren gwamnatin tarayyar.

No comments:

Post a Comment