Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya
a yanzu
Najeriya kasa ce mai johihi 36 da kuma babban birnin tarayya.
A kullum dai ana kara samun cigaba da
sauye-sauye a jihohin domin inganta rayuwar al'ummar da ke zaune.
Shin ko kun san wane jihohi ne suka fi cigaba a Najeriya a shekarar 2019? Ku biyo mu domin ganin ko jihar da ku na cikin jerin wadanda suk yiwa sauran jihohin zarra wurin cigaba.
Abubuwan da ake la'akari da su wajen banbanta jihohi da suka habaka sun hada da ababen more rayuwa, ayyukan yi da makamantansu.
Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu
Ga jerin jihohin namu;
1. Jihar Legas
Tun fil azal, Legas ta dade tana matsayin jihar ta tafi cigaba a Najeriya hakan yasa a kullum miliyoyin mutane suna tururuwa zuwa Legas saboda akwai kamfanoni, masana'antu da tituna da sauransu.
Hakan na nufin kasuwanci na tafiya a garin, ana samun ayyuka kuma masu
saka hannun jari suna zuwa jihar.
Tattalin arzikin jihar Legas ya dara na sauran jihohin Najeriya hakan yasa tayi fice a nahiyar Afirka.
2. Jihar Kano
Bisa dukkan alamu zai yi wahala a samu jihar da tafi Kano habaka a Arewacin Najeriya.
Ana noma sosai a Kano kuma akan fitar da kayayakin noman zuwa kasashen waje. Ga kuma kasuwanci da kamfanoni da masana'antu da kuma albarkatun mutane.
Kano kuma itace cibiyar kasuwanci a Arewakuma gari ne da ke dadin zama.
3. Jihar Anambra
Jihar Anambra dai bashi da girma idan aka kwatanta shi da sauran jihohin Najeriya sai dai masana suna masa kirari da 'hasken Najeriya' saboda akwai yiwuwar zai yiwa Legas da Abuja
fintinkau a nan gaba.
Baya ga ma'adinai na kasa, jihar tana da kasar noma mai kyau wadda kamfanonin masu sarrafa kayayakin noma za su iya amfana dashi domin habaka jihar.
4. JIhar Abia
Jihar Abia cibiyar kasuwanci ne saboda kasuwar Aba ta shahara a duk Najeriya. Kazalika, jihar tana da iskar gas da danyen man fetur.
Mafi yawancin mazauna garin manoma ne yayin da wasu daga cikinsu suna aiki a kamfanoni daban-daban.
5. Jihar Rivers
JIhar Rivers tana daya daga cikin jihohin da suka bunkasa a Najeriya saboda akwai namun daji masu ban sha'awa da tsirai. Jihar kuma tana da tsirai da dabobi masu wahalar samu a sauran jihohi.
Akwai kuma ababen more rayuwa da
guraben aiki a jihar.
6. Jihar Enugu
Jihar Enugu wuri ne da mutum zai iya fara
sana'arsa ko makaranta ko kuma yawon
shakatawa. Babban binrin jihar yana da iyaka da manyan kasuwanci biyu wato kasuwar Onitsha da Aba.
Jihar Enugu kuma tana da yanayi mai dadi wato babu tsananin rana ko tsananin sanyi.
7. Jihar Akwa Ibom
Akwa Ibom tana makwabtaka da jihohin Abia da Rivers. Jihar ta habaka sosai saboda suna da danyen man fetur da iskar gas. Hakan yasa akwai masana'antu da kamfanoni da yasa al'umma ke son zuwa jihar. Bugu da kari, jihar tana da tashar jirgin ruwa, filin tashin jiragen sama.
8. Jihar Ogun
Jihar Ogun kusa ya ke da jihar Legas da ke farko a jerin jihohin mu. Jihar Ogun tana da kamfanoni da masana'antu masu yawa musamman ga kwararun mutane. Hakan yasa jihar take daya daga jihohin da mutum zai iya tafiya domin samun aiki.
9. Jihar Oyo
A jihar Oyo ne aka fara kafa jami'a a Najeriya kuma jihar tana da iyaka da jihohin Kwara, Osun, Ogun da jamhuriyar Nijar.
Akwai makarantu masu yawa a jihar,
musamman jami'o'i wadda hakan yasa mutane da dama suke zuwa jihar. Akwai kuma kasar noma mai kyau a jihar sannan yanayin jihar ya dace da noman Cocoa, Shinkafa, Masara, Gero, Ayaba da sauransu.
10. Jihar Kaduna
Jihar Kaduna tana kusan tsakiya Najeriya ne, Jihar tana da makarantu da cibiyoyin bincike da kuma asibitoci sannan 'yan kasuwa suna cabawa saboda yawan al'umma.
Babban birnin jihar, Kaduna babban gari ne da matafiya suke shige da fice a ko yaushe domin akwai hanyoyi masu kyau da layin dogo, ba abin mamaki bane saboda jihar ke babban birnin yankin Arewa a lokacin turawan mulkin mallaka na Ingila.
No comments:
Post a Comment