Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in
Kasar nan, JAMB ta bayyana cewa mutane
biyu ba za su iya amfani da layin waya daya ba wajen yin rajistan jarabawar ba.
Jami’in hukumar Fabian Benjamin ya sanar da haka wa Gusauloaded ranar Alhamis.
Benjamin ya bayyana cewa mutane biyu ba za su iya amfani da layin waya daya ba saboda duk lambar da mutum ya yi amfani
da shi wajen rajista da shi ne hukumar za ta yi amfani da wajen sadar da sakonin game da jarabawan da kuma samun shiga jami’a.
Ya ce JAMB ta dauki wannan mataki ne
domin kawar da matsalolin rudani a
aiyukkan su sannan da kawar da satan amsa a jarabawar.
” Duk wanda ya yi amfani da lamba ya siya
fom sannan wani dan uwansa ya yi kokarin amfani da lambar na’urar mu ba zai dauka ba.
Benjamin ya ce dalibai za su iya canja
lambar wayar su a lokacin da suke yin
rajista idan har wanda suka fara amfani da
shi ya bace ko kuma an sace wayar.
Ya kuma ce duk dalibin da ya sami matsala wajen yin rajistar zai iya zuwa babbar ofishin su dake Abuja domin warware matsalar sannan dalibin zai iya rubuta jarabawar a ofishin su da zarar an kammala warware matsalar.
A karshe Benjamin yace za a fara siyar da
fom da yin rajista daga ranar 10 ga watan
Jainairu zuwa 21 ga watan Faburairu.
Sannan za a rubuta jarabawar daga ranar
Asabar 16 ga watan Maris zuwa ranar 23 ga watan Maris.
No comments:
Post a Comment