Sunday, January 13, 2019

[SIYASA] BUHARI ZAMUYI A ZABEN SHUGABAN KASA AMMA BAMU BA A.P.C A ZABEN GWAMNA - INJI OKOROCHA




Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya
sanar da dandazon magoya bayan jam’iyyar APC a garin Imo cewa gaba daya mutanen jihar sun yanke shawarar sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa mai zuwa.

” Mu a jihar Imo Buhari zamu zaba a zaben
shugaban kasa, amma zaben gwamna kuwa ba za mu zabi APC ba domin haka kawai wani ba zai zo ya kakaba mana dan takara ba ba. 

Saboda haka mun riga mun yanke
shawarar mu tuni.

Okorocha ya kara da cewa an samu ci gaban da ba a taba samun irin sa ba a jihar tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999.

” Bayan wannan ci gaba da aka samu, akwai dayawa da aka samu a wasu sassan yankin Kudu Maso Gabas da ada babu irin su.

Ita kuwa uwargidan shugaban Kasa, Aisha
Buhari a na ta jawabin, kira tayi ga mata da
matasa da su tabbata sun zabi jam’iyyar
APC da shugaba Buhari domin ci gaba da
kwankwadar romon dimokradiyya da suke
sha a yanzu.

Uwargidan mataimakin shugaban Kasa, Dipo Osinbajo ce ta wakilci Aisha Buhari a
wannan gangami.

Wannan gangami shine na farko wanda
bangaren kamfen din mata da matasa da
uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta
kaddamar a makon da ya gabata.

No comments:

Post a Comment