Sunday, January 13, 2019

[SIYASA] KADAINA YIWA BUHARI SHARRI - FADAR SHUGABAN KASAN TA GARGADI ORTOM





Fadar shugaban kasa tayi kira ga gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, da ya mayar da hankali a kan kokarin warware matsalolin da jihar sa ke ciki, ba ya dinga yawo yana yada karya a kan shugaba Buhari ba.

A sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce, "muna da masaniyar cewar gwamna Ortom na ziyartar Cocin jihar sa tare da fadawa jama'a cewa shugaba Buhari nada shirin musuluntar da Najeriya.

" Da wannan zance na shirme yake yawo yana yakin neman zabe saboda bashi da abinda zai nuna a matsayin aikin da
ya yiwa jama'a.

"Rashin adalci ne ga gwamna Ortom ya fadi haka a kan Buhari, musamman idan l aka yi la'akari da irin goyon baya da gudunmawa da ya samu daga gwamnatin tarayya lokacin da rigingimu makiyaya da manoma suka addabi jihar Benuwe," kamar yadda jawabin ya kunsa.

Buhari da Ortom Jawabin ya kara da cewa, " ba don goyon bayan shugaba Buhari a kan a bar Ortom ya kawo duk tsarin da yake so a Benuwe ba, da bai sukunin kaddamar da dokokin da ya kirkira ba."

Kazalika fadar ta shugaban kasa ta gargadi Ortom da ya guji yiwa Buhari sharri tare da yin kira ga jama'ar jihar Benuwe da kar su bari ya yaudare su da wadannan karairayi.

" Ku tambaye shi me yasa ya kasa biyan albashin ma'aikata da kudin 'yan fansho da kuma abinda ya yi da kudin rarar danyen mai da ya karba daga gwamnatin tarayya, " a cewar jawabin.

No comments:

Post a Comment