Sunday, January 13, 2019

[SIYASA] MURNA A A.P.C YAYIN DA DAN TAKARAR GWAMNA NA P.D.P YA SAUYA SHEKA A JIGAWA


- Wani jigon PDP Alhaji Baba Aliyu Santali, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki

- Santali ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar Jigawa a karkashin babbar jam’iyyar adawar kasar

- Yace ya yanke shawarar hakan ne sakamakon tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a fadin kasar

Wani dan takarar kujerar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Baba Aliyu Santali, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Da yake kaddamar da hakan a bainar jama’a, Alhaji Baba Santali yace ya yanke shawarar hakan ne sakamakon tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a fadin kasar.

wanda ya kasance kwamishinan aiki da
sufuri na tsawon shekaru takwas a karkashin tsohon Gwamna Sule Lamido, yayi bayanin cewa da gangan ya bari sai a karshen zangon APC na farko sannan ya bayyana kudirinsa saboda kore zargin da wasu za suyi kan cewa don a bashi
mukami ne ya koma jam’iyyar.

Santali yace ya dade yana goyo bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari tunda aka kafa kungiyar ‘The Buhari Organisation (TBO).’

Santali ya sauya sheka ne tare da wasu
shugabannin PDP daga mahaifar mataimakin shugaban PDP a yankin Arewa, Ambassador Ibrahim Kazaure.

No comments:

Post a Comment