Tuesday, January 8, 2019

[LABARAI] ATIKU ZAI IYA SAYAR DA NIGERIA IDAN AKA ZABESHI - INJI ADAMS OSHIMOLE

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya yi
kira ga 'yan Nijeriya da su kauracewa zaben dan takarar
shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar inda
ya ce zai sayar da Nijeriya in aka zabe shi a matsayin
shugaban kasa. Oshiomhole yakara da cewa PDP ce silar
matsin tattaalin arzikin da 'yan kasa ke ciki dan haka kada su
kuskura su sake zaben jam'iyyar a yayin zaben shugaban
kasa da zai guduna a ranar 16 watan Feburarun 2019.
Oshiomhole ya fadi hakan ne a shekaran jiya Juma'a a yayin
taron kaddamar da yakin neman zaben Gwmnan jihar Filato
wato Simon Lalong a karo na biyu da ya gudana a filin
wasan mosta jiki na garin Rwang Pam dake Jihar ta Filato.

No comments:

Post a Comment