Tuesday, November 27, 2018

[LABARAI] ZAMFARA TA DAKATAR DA HAKIMAI HUDU





Kwamishinan kananan hukumomin jihar
Zamfara Bello Dankande ya bayyana cewa
babban dalilin da ya sa gwamnati ta dakatar da wasu hakimai hudu a jihar shine zargin da take musu da hannu a ayyukan ta’addanci a jihar.

Hakiman da aka dakatar sun hada da
hakimin Gora dake karamar hukumar
Talatan Mafara, da hakimin Barikin Daji.

Sannan akwai kuma hakimin Gyado da
Tungan Dutsi dake karamar hukumar Bukuyum. 

Dankande ya ce dukkansu za su bayyana a
gaban kwamiti domin wanke kansu daga
wannan zargi da ake musu.

Ya kara da cewa duk wanda aka samu da
laifi zai dandana kudar sa sannan za a cire
shi daga kujerar sarauta da yake kai.

No comments:

Post a Comment