Friday, January 11, 2019

[LABARAI] ANA KYASHE KYASHIN SAUKE SHUGABAN EFCC IBRAHIM MAGU DAGA KUJERARSA






Mun fara jin labari cewa akwai yiwuwar a sauke mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Ibrahim Magu daga kan kujerar sa kwanan nan. 

Shugaban kasa Buhari na shirin sauke Magu daga shugaban EFCC

A jiya ne aka rahoto cewa babu mamaki Ibrahim Magu ya bar mukamin sa na shugaban EFCC, yayin da ake shirin tura sa karatu domin ya kara samun gogewa wajen aikin sa na ‘Dan sanda inda yanzu yake matakin kwamishina.

Jaridar Vanguard tace fadar shugaban kasa tana tunanin aika Magu zuwa kwas, wanda hakan zai bada dama a nada wani ya maye gurbin sa a EFCC. Wani babban jami’i a fadar shugaban kasar ne ya fara kyakyawasa wannan.

Kamar yadda majiyar ta bayayana, shugaban hukumar zai tafi wata makaranta da ake horas da manyan ma’aikatan gwamnati ne domin ya kara samun gogewa a aiki. Tun farko dai dama majalisa ba ta amince da nadin Ibrahim Magu ba.

Idan dai har shugaban kasa Muhammadu Buhari bai canza shawara ba, akwai matukar yiwuwar a nada wani sabon shugaba a hukumar ta EFCC wanda zai jagoranci yaki da rashin gaskiyar da gwamnatin nan ta ke kokarin yi inji rahoton.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi
Osinabjo yana cikin wadanda ke ba Ibrahim Magu kariya a gwamnatin nan. Sai dai duk da irin kokarin shugaban na EFCC, bisa dukkan alamu, maganar tsige sa dada kujerar sa tayi nisa.

A shekarar bara kurum, EFCC ta yi nasarar
daure mutane 317 da aka kama da laifi, kamar yadda shugaban hukumar ya fada. Shi dai mai magana da yawun bakin Magu watau Tony Amokeodo yace bai san da shirin tsige Shugaban ba.

No comments:

Post a Comment