Allah abin tsoro, duniya kasuwa mai ci tana tana tashi. Hafsat Shehu tana daga jerin kyawawan matan industry, matsawar ana batun kyawawan mata to Hafsat Shehu tana ciki.
Tun bayan rasuwar mijinta Ahmed S Nuhu aka daina jin labarin jaruma Hafsat Shehu.
To da yake waiwaye adon tafiyane shine dalilin da yasa mu bin ciko labari inda Hafsat Shehu ta boye tun bayan rasuwar mijinta Ahmed S Nuhu.
Hafsat Shehu tana raye cikin kwanciyar hankali da lumana. Domin yanzu haka tana makaranta ci gaba da karatun ta.
Mun zanta da ita ta wayar salula, acikin
tattaunawar da muke yi da itane ga sanar mana halin da take ciki.
A cewar Hafsat Shehu: gaskiya yanzu rayuwata ta sauya ba kamar shekarun baya ba.
A baya nayi rayu tareda mijina amma yanzu rayuwa nake daga ni sai halina.
Yanzu haka ina ci gaba da karatuna kuma na kusa kammalawa.
Ya maganar aure idan an gama makaranta?
Gaskiya tun da na rasa Ahmed bana tunanin wani aure yanzu.
Amma da yake ni musilmace dole inyi aure.
Dan haka yanzu ma akwai wanda iyayena suke so na aura kuma nima yayi min.
Na ji kamar kina kuka menene dalilin zubar
hawayenki?
Wallahi duk lokacin da akayi maganar aure sai na tuna da tsohon mijina wanda zuciyata take so da kauna.
Amma mutuwa tayi mana yankan kauna.
To mun gode Allah domin wanda ya dauke shi {Allah} ya fi ni son Ahmed.
Yanzu idan kin tashi yin aure wanne irin miji ki ka fi so?
Ni kowanne kala inaso, matsawar yana sona da gaskiya. ba ruwana da kudinsa ko kyan fatarsa matsawar yana da tsafta da rikon addini to ina maraba da shi, koda kaine.
Ni kuma Hafsat? Me hakan ke nufi?
Ji nayi ka damu da maganar aurena nasani ko kawata zaka yi kishiya mu zama mu uku kenan.
Dariya mukayi ni da ita. Haffsat macace mai barkwanci da yawan son raha. Yanzu atakaice Hafsat Shehu tun rasuwar mijinta ba ta kuma yin aure ba.
Ta kama mutuncin kanta bata shigar banza bare ayi mata fassara ta daban.
No comments:
Post a Comment