jin dadin murza-leda karkashin kocin rikon kwarya Ole Gunner Solskjaer.
Hulda tsakanin Pogba da Jose Mourinho ta yi tsami, inda yake ajiye dan kwallon Faransa a benci, har da wasan da Liverpool ta doke United a watan Disamba.
Bayan wasan ne United ta sallami Mourinho ta kuma nada Solskjaer kocin rikon kwarya zuwa karshen kakar 2018/19
Pogba ya dawo kan ganiyarsa karkashin Solskser wanda ya horas da shi a matasan United, yanzu kuma ya ba shi damar yin yadda yake so a cikin fili.
Hakan ne ya bai wa Pogba damar cin kwallo hudu ya kuma bayar da hudu da aka zura a raga, har da wadda ya bai wa
Marcus Rashford ya ci Tottenham a ranar Lahadi.
United ta ci wasa shida a jere da kocin rikon kwarya Solskjaer ya ja ragamarta a karon farko, kuma biyar a gasar Premier.
Kungiyar tana ta shida a kan teburi da maki 41 iri daya da wanda Arsenal ta ke da shi mai mataki na biyar a teburin Premier.
No comments:
Post a Comment