Monday, January 14, 2019

[SIYASA] DA BAN GOYAWA BUHARI BAYA BA DA BAI CHI ZABE BA A ZABEN 2015 - TSOHON SHUGABAN KASA OBASANJO


Da Ban Goya Wa Buhari Baya Ba Da Bai Samu Nasarar Cin Zaben 2015 Ba – Obasanjo

Daga nan har karshen rayuwata Buhari zai ci gaba da kira na da sunan Yallabai A ranar Laraba ne tsohon shugaban kasar Nijeriya, Chief Olusegun Obasanjo, ya ce da bai goyi bayan Buhari ba a zaben 2015 da bai lashe zaben ba. 

Bayan nan Obasanjo ya ce shi ne babban wanda ya cancanci ya soki gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

Yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro wanda gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun da sauran manyan mutane suka
halarta, Obasanjo ya ce, "Na san wane Buhari, shi ma ya san wane ni. 

Daga nan har karshen rayuwata Buhari zai ci gaba da kira na Yallabai. Da ban goya masa baya ba a 2015 da bai samu nasara ba. 

Ina da ilimi da gogewar da zan masa gyara. 

Bai kamata a ce Nijeriya tana matakin da take a yanzu ba. 

Nijeriya za ta iya fin haka. Allah ya riga ya bamu dukkan abin da muke bukata. "Ina da cancantar da zan soki Buhari. 

Na farko, na mulki kasar nan kafin shi. Na biyu, na zubar da jinina saboda kasar nan. 

Hatta dan cikina ma ya zubar da jininsa. Saboda me to ba zan iya magana a kan abin da fi cancanta ga kasar nan ba? Ni na fi cancanta da aikata haka.

No comments:

Post a Comment