Sunday, October 21, 2018

[SIYASA] Za a shiga Kotu da Abba Yusuf a game da takarar Gwamnan Kano


Mun ji cewa Daya daga cikin ‘Yan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP Jaafar Sani-Bello ya shigar da kara a gaban Kotu inda yake kalubalantar takarar Abba Kabir Yusuf a zabe mai zuwa na 2019.

Jafar Sani-Bello ya maka Abba Yusuf kara a gaban Kotu Source: FacebooK 

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana wannan a makon da ya gabata inda tace ‘Dan takarar yana karar Hukumar zabe na kasa watau INC da kuma kwamitin Jam’iyyar sa ta PDP da ta gudanar da zaben da ‘Dan takarar Kwankwaso yayi nasara. 

Alhaji Jaafar Sani-Bello ya shigar da kara ne a babban Kotun Tarayya da ke Kano inda yake neman ya ji dalilin da ya sa Kwamitin Ezeoho Onua da Danlami Abdulhamid ta amince da zaben fitar da gwani na takarar Gwamna a PDP da aka yi. ‘

Dan takaran yace Injiniya Abba Yusuf bai sauya-sheka daga APC ba yayi takara a PDP wanda hakan ya sabawa doka. A dalilin haka ne Sani-Bello ya nemi Kotu ta tsaida sa a matsayin ‘Dan takara domin zaben Abba da aka yi bai da inganci. Read more:

Alhaji Sani-Bello ya nemi babban Alkalin Kotun mai shari’a AT. 

Badamasi ya tsaida shi a matsayin ‘Dan takara ganin cewa shi ya zo na biyu a zabe. Yanzu dai Kotu za ta fara zama a Ranar Alhamis 25 ga wannan wata domin warware matsalar. 

A zaben fitar da gwanin da aka yi, Ezeogu Onouha, ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ne yayi nasara da kuri’a 2, 421 yayin da Jafar Sani-Bello ya samu kuri’a 1,258. Sani Bello yace akwai wala-wala a zaben don haka a dakatar da Yusuf daga takara.

FOLLOW US ON INSTAGRAM

FOLLOW US ON TWITTER

JOIN OUR WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment