Sunday, October 21, 2018

[LABARAI] Matasan kudancin Kaduna sun ci alwashin kayar da El-Rufa'i zabe

- Matasan yankin Kudancin Jihar Kaduna sun dau alwashin hambarar gwamna jihar Mallam Nasir El-Rufai a 2019 

- Matasan karkashin kungiyar Southern Kaduna Youths For Progress and Development sunyi alkawarin jefa kuri'unsu ga dan takarar jam'iyyar PDP a jihar

- Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar shine Alhaji Isa Ashiru yayin da mataimakinsa kuma shine Sunday Katung

A yayinda babban zabe na shekarar 2019 ke karatowa, matasa daga Kudancin jihar Kaduna karkashin kungiyar Southern Kaduna Youths For Progress and Development sun dau alwashin hambarar da gwamna Nasir El-Rufai daga kan kujerarsa. 

Kungiyar ta bayar da wannan sanarwar ne a sakatariyar kungiyar 'yan jarida na Najeriya reshen jihar kamar yadda Punch ta ruwaito.

2019: Matasan Kudancin Kaduna sun bayyana tanadin da suka yiwa El-Rufai Source: Depositphotos 

Gusauloaded.com.ng ta gano cewar 'ya'yan kungiyar sunyi alkawarin marawa Alhaji isa Ashiru na jam'iyyar adawa da mataimakinsa Sunday Katung baya idan zaben ta zo. Ciyaman din kungiyar, Danjuma Sarki ya jadada cewar kungiyar za ta kawo kuri'u daga kananan hukumomi 11 da ke yankin Kudancin Jihar.

 "A wannan lokacin da jihar mu ke bukatar zaman lafiya, hadin kai da jagorancin na gari, Ashiru da Katung ne za su kawo dauki ga al'ummar jihar Kaduna," inji shi

A wani rahoton, Gusauloaded.com.ng ta ruwaito cewar shugaban kungiyar Kwadago na kasa (NLC), Ayuba Wabba ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi gwamna Nasir El-Rufai kan ingiza sauran gwamnonin jihohin Arewa su kori malaman makarantu daga aiki.
FOLLOW US ON INSTAGRAM

FOLLOW US ON TWITTER

JOIN OUR WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment