Sunday, October 21, 2018

[LABARAI] An kashe mutane 8 a cikin gona a Kauyen Molai da ke daf da Maiduguri

Labari na zuwa mana dage manema labarai cewa ‘Yan ta’addan nan na Kungiyar Boko Haram sun kai sababbin hare-hare a wani Kauye da ke kusan da Garin Maiduguri inda su ka kashe mutane da-dama.

Boko Haram sun kashe mutane da dama a Kauyen Molai Source: UGC

Kusan wasu manoma 10 ne su ka bakunci lahira a lokacin da ‘Yan Boko Haram su ka shiga Kauyen Molai da ke cikin Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno. ‘Yan ta’addan sun kase jama’a ne yayin da su ke aiki a cikin gonakin su. 

Bayan kisan da ‘Yan ta’addan su kayi, sun kuma raunta mutane sama da 15 a wannan Kauye da ke daf da Birnin Maiduguri. ‘Yan ta’addan sun zo a motoci 2 ne dauke da makamai irin su adda da gatari su ka shiga sarar Bayin Allah.

Yanzu dai an tsince gawa 12 a cikin dajin na mutanen da aka aika lahira. Wani Bawan Allah da yake garin mai suna Babakura Kolo ya bayyanawa ‘Yan Jarida wannan. Wasu monoman dai sun samu munanan rauni ne a harin. 

Bangaren Abubakar Shekau na ‘Yan ta’addan ne aka sani da irin wannan mugun aiki. Manoman sun yi kokarin tserewa lokacin da su ka hangi ‘Yan ta’addan amma aka nemo su aka kashe babu gaira babu dalili.
FOLLOW US ON INSTAGRAM

FOLLOW US ON TWITTER

JOIN OUR WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment