Sunday, October 21, 2018

[LABARAI] Ya kamata Likitocin mu da ke waje su dawo Najeriya domin ayi gyara - Abike Dabiri





Mun ji labari cewa Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin kasar waje Abike Dabiri Erewa ta tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta APC tana da shirin inganta harkar kiwon lafiya a Najeriya.

Mai ba Buhari shawara ta nemi Likitocin Najeriya su dawo gida Source: UGC 

Babbar Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan abubuwa da su ka shafi kasashen ketare ta bayyana cewa Gwamnatin nan za ta cinma wannan buri ne ta hanyar hada-karfi da Likitocin ta da ke aiki a Kasar waje. 

Hon. Abike Dabiri Erewa tayi wannan kira na musamman ne a wajen wani babban taro da aka shirya game da sha’anin kiwon lafiya a cikin Garin Abuja inda tayi magana game da dinbin Likitocin Najeriya da ake da su a ketare.

Abike Dabiri ta nemi manyan Likitocin da ake ji da su a Duniya daga Najeriya da su dawo gida domin su inganta harkar lafiya a kasar su. 

Dabiri tace Najeriya tana da kwararrun ta na kan-ta don haka ba ta bukatar taimako daga waje. Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, wani babban Likitan Kasar Dr Ifeanyi Nsofor yayi jawabi a wajen taron inda yayi irin wannan kira ga Likiticocin na Najeriya da aka aiki a kasashen waje domin ganin an inganta sha’anin lafiya. 

Kwanaki ne Ministan lafiya ya jawo fushin jama’a inda ya nemi wasu Likitocin su koma sana’ar dinki ko nama idan aiki bai samu ba. Ministan lafiyan yace ba dole kowane Likita sai ya zama kwararre a Kasar ba.



FOLLOW US ON INSTAGRAM

FOLLOW US ON TWITTER

JOIN US ON WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment