Tuesday, October 23, 2018

[LABARAI] Baki shi ke yanka wuya: Rabaran Fada Mbaka ya debo ruwan dafa kan sa





Rabaran Fada Mbaka ya debo ruwan dafa kan sa

- Ya sha caccaka daga wani jigo a jam'iyyar PDP 

- Yace kamata yayi malamin addinin ya tsaya matsayin sa na malami 

Fitaccen babban malamin addinin kiristancin nan na Najeriya, Rabaran Fada Ejike Mbaka ya sha caccaka daga wani magoyin bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma masoyin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a 2019,

 Alhaji Atiku Abubakar watau Cif Chinedu Eya.

Baki shi ke yanka wuya: Rabaran Fada Mbaka ya debo ruwan dafa kan sa Source: Depositphotos 

Cif Chinedu Eya daga jihar Enugu ya bayyana cewa shi bai ga dalilin da shi Rabaran din zai rika tsoma bakin sa cikin harkokin siyasar kasar nan tare kuma da cewa shi ba dan siyasa bane, kamar dai yadda majiyar mu ta jaridar Vanguard ta ruwaito mana. 

Gusauloaded.com.ng Hausa ta samu cewa caccakar ta Cif Chinedu Eya ga malamin addinin na zuwa ne kwanaki kadan bayan an ruwaito yayi wata magana game da 'yan takarkarin na shugaban kasa a jam'iyyar ta APC da PDP a shekarar 2019. 

An dai ruwaito Fada Mbaka yace wai shi dai Buhari shi ne Canji na gaskiya yayin da shi kuma Atiku yake tamkar 'yan canjin kudi - inda ya alakanta zaman Atiku dan takarar shugaban kasa na PDP da irin kudaden da ya kashe wajen zaben.



FOLLOW US ON   INSTAGRAM

FOLLOW US ON TWITTER

JOIN US ON WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment