Sunday, October 21, 2018

[SIYASA] Kasashen waje su na cike da mamakin yadda Atiku zai yi takaran Shugaban kasa - Lai Mohammed




- Lai Mohammed yace Gwamnatin APC ba za ta karkata daga kudirin yaki da barna ba 

- Ministan labaran ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da aka yi a Birnin Landan 

- Yace tsayawa takaran Atiku ya ba Duniya mamaki saboda tambarin satar da ke kan sa 


Lai Mohammed yace kasashen waje su na mamakin yadda Atiku zai yi takara Source: Depositphotos 

Ministan yada labarai da na al’adun kasar nan Lai Mohammed ya bayyana cewa Duniyar kasar waje ta na mamakin yadda Alhaji Atiku Abubakar ya samu tikitin takara a Jam’iyyar PDP a Najeriya duk da kashin da ke jikin sa. 

Lai Mohammed yace jama’ar kasar waje sun yi mamakin hakan ne ganin yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ta ke yaki da barna a Najeriya. Ministan labaran ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da aka yi a Birnin Landan.

Minista Alhaji Lai Mohammed yace jama’a su na ta tambayar sa yadda mutumin da ake zargi da sata irin Atiku ya samu kujerar takarar Shugaban kasa a zaben 2019 alhali ana kokarin yaki da barayi a wannan lokaci a Kasar. 

Mohammed yace har ya rasa amsar da zai ba jama’a ganin cewa babu wanda ya san inda Atiku ya samu mahaukatan kudin da ya mallaka. Ministan dai yace ya san cewa ba shakka mutanen Najeriya sun san wanda za su zaba a 2019. 

Lai dai yayi hira da gidajen yada labarai na Reuters, Aljazeera, the Economists, AP, New African, African Business da African Review Magazines a kasar Ingila. Atiku Abubakar ne dai zai kara da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben badi.



FOLLOW US ON  INSTAGRAM

FOLLOW US ON  TWITTER

JOIN OUR  WHATSAPP GROUP

No comments:

Post a Comment