Saturday, October 20, 2018

[SIYASA] Shehu Sani: ‘Na Fice Daga APC Saboda Gwamnoni Sun Fi Karfin Buhari’




Zan sake takarar kujerata a zabe mai zuwa duk da na fice daga APC – Shehu Sani
Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a jihar Kaduna ta Najeriya ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kasar, yana mai cewa gwamnonin jam’iyyar sun fi karfin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanatan ya gaya wa BBC cewa jam’iyyar wadda talakawa ke so da kauna ta kauce daga ainahin akidojinta na saboda gwamnonin jihohin da take mulki sun yi mata kamun kazar-kuku, hatta shugaban kasar ma wanda dan jam’iyyar ne sun fi karfinshi a kanta.
Sai dai kuma duk da cewa Sanatan bai samu tikitin sake takarar kujerar mazabar tasa ba a karkashin APC, ya tabbatar wa BBC cewa tabbas zai yi takarar domin akwai jam’iyyun da suka riga suka tsayar da shi amma bai bayyana su ba, idan lokaci ya yi zai sanar.
Shehu Sani ya alakanta ficewar tasa da yadda aka gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar a jihohi ta yadda sai abin da gwamnoni suka zaba ba jama’a ba shi ne uwar jam’iyyar ma a tarayya za ta amince da shi.
Sanatan ya ce tun a baya ya yi yunkurin ficewa daga jam’iyyar lokacin sauran takwarorinsa ‘yan majalisu suna ficewa, amma uwar jam’iyyar ta dakatar da shi bisa alkawarin cewa za a daidaita al’amura, amma kuma a yanzu alkawarin ya zama kamar yaudara.
Dan majalisar dattawan yana da takaddama da reshen jam’iyyar na jiharsa wanda ke bin bayan gwamnatin jihar a game da tikitinsa na sake yin takarar kujerar a zaben 2019, inda jam’iyyar ta mika sunan mai ba wa gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufa’i shawara kan harkokin siyasa Mallam Uba Sani a matsayin dan takararta.
Kafin hakan hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja tun a baya ta sanar da cewa Shehu Sani shi kadai ne aka wanke da zai yi takarar kujerar, matakin da gwamnatin jihar da reshen jam’iyyar na jihar suka ki amincewa.
Sanata Shehu Sani da gwamna El-Rufa’i daman kusan ba sa ga-maciji da juna tun bayan zabensu a shekara ta 2015, duk da cewa ‘yan jam’iyya daya ne, ta yadda ma har sukan yi amfani da kalamai na batanci ga junansu.

No comments:

Post a Comment