An yi sa-in-sa da kociyan Manchester United Jose Mourinho lokacin da ‘yan Chelsea ke bureden ci na biyu da Ross Barkley ya farke musu a minti na 96 a Stamford Bridge a wasan da suka tashi 2-2.
Mourinho ya harzuka ne bayan da wani daga cikin tawagar jami’an kungiyar ta Chelsea ya biyo ta gabansa da gudu yana murnar rama cin da suka yi bayan wani gumurzu da aka yi a bakin gidan United a lokacin da ana dab da tashi daga wasan.
Rüdiger ne ya fara daga ragar Manchester United minti 21 da shiga fili, har kuma aka dawo daga hutun rabin lokaci kafin sannan Martial ya farke a minti na 55.
Can kuma a minti na 73 ne Martial din ya sake ci wa Manchester United ta biyu, har aka yi ta gumurzu, kusan tashi bayan alkalin wasa ya kara lokaci wajen bakwai saboda tsawon tsaikon da aka samu a cikin fafatawar Chelsea ta rama ta biyu ta hannun Ross Barkley.
Sakamakon ya sa a yanzu Chelsea ta yo kasa daga matsayi na daya zuwa na biyu da maki 21 a wasa tara Manchester City ta zama ta daya, yayin da ita ma Manchester United ta yo kasa zuwa ta tara da maki 14.
No comments:
Post a Comment