Saturday, October 20, 2018

[SIYASA] ATIKU BAZAI IYA KARAWA DA SHUGABA BUHARI A ZABEN 2019 BA - DAGA NASIR EL-RUFA,I
Daya daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki ya ce ba za su rasa bacci ko na dakika guda ba sakamakon ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Atiku Abubakar daga jam'iyyar. Gwamna Nasiru el-Rufa'i na jihar Kaduna ya ce da ma suna sane da shirinsa na barin jam'iyyar. Ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya dauki wannan mataki bayan taron da wasu gwamnoni da suka fito daga yankin arewa suka yi a kwanakin baya-baya nan. Gwamnanonin sun yi kira ga Shugaba Muhammdu Buhari a kan ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019. Shugaban kungiyoyin da ke goyon bayan Atiku Abubakar ya tabbatarwa da ficewarsa daga jam'iyyar, sai dai bai bayyana jam'iyyar da yake son komawa ba tukuna. A wata sanarwa da Atikun ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam'iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa 'yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki. Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman- zamansa jagororin jam'iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam'iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam'iyyarsa ta PDP. Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba. "A kan wannan dalili ne mambobin jam'iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin binkundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci." "A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam'iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam'iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni," a cewar sanarwar. Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Duk jam'iyyar da ba za ta kula da al'amuran matasa ba to matacciyar jam'iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne." A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauya jam'iyyun siyasa.

No comments:

Post a Comment