Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa ya zuwa ranar Talata, jam’iyyun siyasa takwas ne kacal daga cikin jam’iyyu 91 da aka yi wa rajista, suka mika wa hukumar sunayen ‘yan takarar su na zabukan 2019.
Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka jiya Laraba a lokacin da ya ke magana a wurin taro da kungiyoyin sa-ido da kishin jama’a da na dimokradiyya da ke da alhakin kula da yadda ake gudanar da zabe.
Kungiyoyin sun yi taron ne da INEC, inda Yakubu ya kara da cewa ya na sa ran karbar sunayen sauran ‘yan takarar tsakanin Laraba zuwa Alhamis, kasancewa a ranar Alhamis din ce, 18 Ga Oktoba za a rufe karbar sunayen.
Shugaban na INEC wanda ya nuna damuwar rashin kai wa hukumar sa sunayen ‘yan takara da wuri, ya ce Majalisar Tarayya ta amince wa INEC kashe naira biliyan 189 wajen gudanar da zabukan 2019.
INEC na sa ran buga sunayen halastattun ‘yan takara da bayanan jihohin su da mazabun da suka fito, kwanaki bakwai bayan kammala mika mata sunayen da za a rufe a yau Alhamis.
#Rariya
No comments:
Post a Comment