Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya ja Hankalin 'Yan
Jam'iyyar APC Na Jihar Kano akan taba muhibbar duk wani wanda
yake Tafiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Jihar Kano.
Gwamna ya bayyana haka ne yau a wajen Bikin Ranar Matasa ta
Duniya wanda aka Gabatar a dakin Wasa Na Sani Abacha dake
Kofar Mata inda yace Koda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
mutum yake kauna Amma baya kaunarsa to kada a zage shi domin da
shi da Muhammadu Buhari Danjuma ne da Danjimmai don haka kar
a zage shi.
Ya ja Hankalin Matasa akan wasu da ya ji suna zagin masu mukamai
a Gwamnatin Tarayya daga jihar Kano inda ya umarce su da su daina.
SSA Social Media II,Kano
Abubakar Aminu Ibrahim.
Danna Nan Domin Shiga Whatsapp Group Din Mu
No comments:
Post a Comment