Sunday, August 12, 2018

[LABARAI] NIGERIA ZATAYI SALLAR IDI RANAR TALATA - SARKIN MUSULMI



Ganin Wata a Najeriya
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya amince da yin Sallah a Najeriya
tare da Saudia wato ranar talata 21 ga Agusta 2018 bayan tuntubar
manyan Malamai na kasa da Sarakuna.
Bisa ga haka, mutane suna iya fara azumin Dhul Hajji daga yau
lahadi.
A saurari sanarwa daga majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi. Da
kuma sharhi da zamu fitar daga baya in Allah ya so.
Mun sanar da ku ne don yawan wayoyi da ake ta bugowa daga ko ina
ana tambaya.
Allah ya karbi ibadarmu.

Dr Mansur Sokoto


Danna Nan Domin Shiga Whatsapp Group din mu

No comments:

Post a Comment