Monday, February 19, 2018

[SIYASA] JAM'IYYAR APC TA DAKATAR DA GWAMNAN JAHAR KADUNA




APC Ta Dakatar Da El Rufa'i Daga Jam'iyyar Na Tsawon Watannin
Shida A Jihar Kaduna

Bangaren Jam'iyyar APC a jihar Kaduna karkashin jagorancin Alhaji
Danladi Wada, sun bayar da sanarwar dakatar da Gwamnan Jihar
Nasiru El Rufa'i daga Jam'iyyar na tsawon Watannin Shidda, biyo
bayan abinda suka kira taurin kai da rashin martaba dokokin
Jam'iyyar da Gwamnan yake yi.

Da yake gabatar da jawabi a yayin wani taron manema labarai da
bangaren shugabancin Jam'iyyar ya kira a sabon Ofishin Jam'iyyar
dake Titin Sambo Kaduna, mukaddashin Shugaban Jam'iyyar Alhaji
Danladi Wada, yace daukar matakin ya zamo wajibi ne, domin dawo
da Gwamnan cikin hayyacin shi, sakamakon kememe da tozarta
dokokin Jam'iyyar da Gwamnan ya keyi, inda ya bada misali da
takardar da suka aikewa Gwamnan da ita na neman ganawa da shi,
amma El Rufa'I bai zoba, sannan bai turo da wakili ba, wannan shine
dalilin daya sanya suka bada Awanni 48 ga Gwamnan, muddin kuma
bai amsa gayyatar su na zuwa kafin cikar wa'adin ba, to babu shakka
doka za tayi a kanshi, kamar yadda dokokin jam'iyya suka tanada, sai
gashi Wa'adin ya cika ba tare da ganin keyar Gwamnan na, wannan
shine dalilin su na dakatar da Gwamnan har tsawon wannan lokaci.

Shugaban Jam'iyyar ya cigaba da cewar shine halastaccen Shugaban
APC a jihar, kasancewar shi aka zaba a matsayin matakin Shugaban
Jam'iyyar tun farkon kafa ta, lokacin da mataimakin Gwamna
Barnabas Bantex ke matsayin Shugaban Jam'iyyar, saboda haka
tafiyan Bantex bisa ga tsarin doka ya bashi damar zama Shugaba, duk
da cewar El Rufa'I yayi gaban kanshi ta hanyar nada wani jeka nayi
ka a matsayin shugaba, inda ya tabbatar da cewar uwar Jam'iyyar ta
kasa shugabancin shi ta sani, saboda haka yana da damar zartar da
hukuci muddin bai sabawa dokokin Jam'iyyar ba, kuma abinda yayi
amfani dashi kenan ya dakatar da El Rufa'I.

Jam'iyyar APC a jihar Kaduna dai ta shiga cikin wani rudani tun
bayan shelanta bude sabon Ofishin Jam'iyyar da bangaren Sanata
Suleiman Hunkuyi su kayi, inda a ranar farkon zama a Ofishin aka
bada sanarwar dakatar da Uba Sani mai taimakawa El Rufa'I ta
fuskar siyasa, 'yan kwanaki kadan sai bangaren APC masu biyayya ga
Gwamna suma suka kira taro inda suka bayyana dakatar da Sanata
Hunkuyi da dukkanin 'ya'yan APC masu adawa da Gwamnan, lamarin
da ya sanya ake ganin cewa shine dalilin yin wani taro da bangaren
APC Masu adawa da El Rufa'I suka gaudanar, inda suka shelanta
dakatar da Gwamnan na tsawon Watannin shidda.

No comments:

Post a Comment