Saturday, February 10, 2018

[LABARAI] SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAYI TAKADE DA RAI-RAYA A BANGAREN SHARI'AH





A sakamakon shawarwarin da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a
ta Kasa ta bayar kan alkalan da aka zarge su da aikata laifuka a
bakin aiki, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da
korar Maishari’a O.O Tokode da kuma ritayar tilas ga Alkali
Adeniyi Ademola, dukkansu alkalai a manyan kotunan tarayya.

Kafin yanke wannan hukuncin, Alkali Ademola ya yi alkalanci ne a
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, yayin da shi kuma Maishari’a
Tokode ya yi a Babbar Kotun Tarayya da ke Benin.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba
Shehu ya raba wa manema labarai jiya a Abuja, ta bayyana cewa
an dauki matakin ne bisa tanade-tanaden da ke sashe na 292,
karamin sashe na 1, a karkashin sashe na biyu (b) na Kundin
Tsarin Mulkin Nijeriya da aka yi wa kwaskwarima.

Sanarwar ta yi hannunka-mai-sanda ga sauran alkalan da ke
bakin aiki inda ta ce: “Shugaban kasa yana kira ga alkalai su yi
aikinsu bilhakki da gaskiya tare da kauce wa karbar cinhanci da
rashawa a bakin aiki”.

Malam Garba Shehu, ya kuma fitar da wata sanarwa ta daban
wadda ta bayyana cewa, “ana kan bin matakan tabbatar da cewa
mutane, manyan alakalai da kanana da Majalisar Kula da Harkokin
Shari’a ta Kasa ta aika sunayensu a nada su aiki a kotuna daban-
daban sun cancanta, kuma ba su da wani nakasu a kan aikin
alkalanci”.

In ji sanarwar.
Malam Garba Shehu, ya yi bayanin cewa matakin da shugaban
kasan ya dauka a kan nade-naden alkalan, karfin iko ne da sashe
na 5 na tsarin mulkin shekarar 1999 ya bashi, wanda a karkashi
aka bashi damar yin hakan tare da la’akari da duk abubuwan da
suka kamata.

“Muna tabbatar wa ‘Yan Nijeriya cewa Shugaba Buhari zai nuna
amincewarsa ko akasain haka da zarar an kammala tantancewa”.

Idan za a iya tunawa dai, a taron da Majalisar Kula da Harkokin
Shari’a ta Kasa ta gudanar a ranar 6 ga Disambar 2017 ne ta ba
da shawarar a yi wa Maishari’a Ademola da Maishari’a Tokode
ritayar dole saboda nuna rashin da’a a aikin alkalanci.

Amma kuma majalisar ta ce, Ademola ya mika mata takardar
sanarwar ritayarsa daga aiki tun a watan Oktoban 2017, sabanin
ranar 9 ga Afrilun 2018, lokacin da ka’idar ritayarsa daga aiki za
ta cika saboda ya cika shekara 65 yana aiki.

Ta kara da cewa, ta ba da shawarar a yi masa ritayar dole ce a
sakamakon binciken da majalisar ta yi game da zargin da aka yi
masa a cikin takardar koken da wasu mutum takwas suka rubuta a
kansa, a karkashin kwamitin ‘yanmajalisar wakilai na Jihar
Anambara na jam’iyyar PDP.

Kwamitin mutanen ya zargi Maishari’a Ademola da nuna son-kai
a wata shari’ar da ya yi kan zaben 2015 wanda ya gaggauta yanke
hukunci saboda alakar jini da ke tsakaninsa da wanda ya kai kara•

Har ila yau, sun zarge shi da kin karanta wani sakin-layi daga
cikin rubutaccen hukuncin da ya basu a gaban kotu kowa ya ji; tare
da badda-bamin wata jumla, da masu koken suka nemi a sake duba
su da idon basira a kotun daukaka kara lokacin da suka shigar da
kara a gabanta•

Haka nan, sun ce akwai alamomin tambayoyi kan kwane-kwanen
da maishari’an ya yi a cikin hujjoji da dalilan da ya bayar na
hukuncin da ya yanke a kan shari’ar•

Bugu da kari, sun kuma zarge shi da kara yawan lokacin yanke
hukuncin zuwa wata biyar maimakon wata uku da doka ta kayyade.

Duk da kasancewar masu koken sun janye zarge-zargen da suka yi
wa Maishari’a Ademola, dokar ladaftarwa ta 16 ta Majalisar
Harkokin Shari’ar, ta same shi da laifin kin yanke hukunci a daidai
lokacin da aka ka’idance wanda yake nuna rashin da’a a bakin aiki.

A cewar majalisar, wannan laifi ne bisa tanadin sashe na 292,
karamin sashe na 1, a karkashin sashen na biyu (b) na Kundin
Tsarin Mulkin Nijeriya.

Dangane da batun Maishari’a Tokode kuwa, Majalisar Kula da
Harkokin Shari’ar ta ayyana cewa ta ba da shawarar a yi masa
ritayar dole ne ba tare da bata lokaci ba, a sakamakon binciken da
ta yi kan koken da Kungiyar Fafutukar Tabbatar da Rikon Amana
da Gaskiya kan Sha’anin Kudi (SERAP), da kuma wanda
Abimbola Awogboro suka gabatar mata.

Majalisar ta ce, masu koken sun zargi Maishari’a Tokode da
karkatar da hankalin Hukumar Kula da Sashen Shari’a ta Tarayya
da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa, ta hanyar mika
musu hukunce-hukuncen shari’o’i guda shida da ya yi ikirarin cewa
shi ya yi a lokacin da yake aikin Lauya, a matsayin wani bangare
na cika ka’idar nada shi babban jami’in shari’a kuma ya samu
nasara aka nada shi.

“Sai dai kuma, daga bisani kwamitin binciken da majalisar ta kafa
ya gano cewa shari’a daya ce kawai ya yi hukunci a kai daga cikin
hukunce-hukuncen shari’o’i shida da ya mika”, in ji majalisar.

Bayan korar da aka yi wa Maishari’a Tokode, har ila yau zai
amayo dukkan kudaden albashi da alawus-alawus da aka biya shi
tun daga ranar 2 ga Disamban 2015 da aka rantsar da shi a
matsayin Alkalin Babbar Kotun Tarayya har zuwa yau.

Wasu ‘Yan Nijeriya na ganin matakin da Shugaba Buharin ya
dauka a matsayin kwakkwarar hanyar gyara sashen na shari’a ya
dawo kan turbar kima da martabar da aka san shi da su tun tale-
tale.

Sannan za si zama izina ga masu ha’inci a cikin ayyukansu na
shari’a.

#hausaleadership

No comments:

Post a Comment