Tuesday, February 6, 2018

[LABARAI] AN KAMA DAYA DAGA CHIKIN MASU SAFARAR MAKAMAI ZUWA BENUE

An Kama Mai Safarar Makamai Zuwa Jihar Benue
Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Jigwa
sun kama wani da ya yi odar makamai zai kai jihar Benue.
Mataimakin kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Jigawa, Oko
Micheal shi ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Talata a
garin Dutse babban birnin jihar Jigawa.
Mista Oko ya kara da cewa jami'an su suna kan aiki ne a daidai titin
Jahun-Gujungu a yayin da suka kama mutumin.
"Wanda ake zargin mai suna Salisu Mahamouda an kama shi ne a
ranar Lahadi (4-2-2018) tare da bindigu guda biyu da harsashai",
inji Mista Oko.
Hukumar ta NDLEA ta ce nan bada jimawa ba za ta mika mutumin
da makaman ga hukumar 'yan sanda domin ci gaba da gudanar da
bincike.
Wanda ake zargin, Salisu Mahmouda ya bayyana cewa shi dan asalin
jihar Kaduna ne. Sannan ya yi karatu a jihar Nassarawa, inda daga
bisani ya koma harkar safarar makamai tsakanin jihar Nassarawa da
Benue.

No comments:

Post a Comment