Wednesday, January 16, 2019

[LABARAI] ZA'A FARA ATISAYEN OPERATION PYTHON DANCE A MAIDUGURI

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za a fara atisayin ‘Operation Python Dance’ a Maiduguri jihar Barno.

Jami’in rundunar Abdulmalik Biu ya sanar
da haka a taron kadamar da atisayin inda ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ta
shigo da wannan atisayin a shekaran 2018 a kasar nan domin kama masu aikata miyagun aiyukka.

Ya ce rundunar za ta fara atisayin ne daga
yanzu zuwa ranar 28 ga watan Faburairu.

” Wannan atisayi ana yin sa ne domin samar da zaman lafiya da kare rayuka da
dukiyoyin mutane musamman a yanzu da
zaben 2019 ya tunkaro.

Sannan muna gargadin matasan da ke
aikata ayyukan ta’addanci da su kwana da
shirin kuka da kan sa domin sai ya dandana kudar sa.

No comments:

Post a Comment