Wednesday, January 16, 2019

[LABARAI] MUTANE MILIYAN 2.5 NE ZASUYI ZABE A JAHAR FILATO


Mutane miliyan 2.5 ne za su yi zabe a jihar Filato


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa
(INEC) akalla mutane miliyan 2 da rabi ne
suka yanki rajistar kada kuri’a a zaben 2019 da za a fara gudanarwa cikin watan
Fabrairu mai zuwa a Jihar Filato.

Kwamishinan INEC mai kula da jihohin
Filato, Nija, Kaduna da FCT, Antonia
Simbine, ce ta bayyana haka a wani taron
wayar da kai a jiya Talata a Jos.

Ta ce daga cikin adadin akwai kashi 50.6
wadanda mata ne, sai kuma 47.3 maza ne.
Ta kuma yi kira ga wadanda suka yi rajista
amma ba su kai ga karbar katin rajistar ba
da su hanzarta zuwa su karba.

Sannan kuma ta kara nanata cewa INEC ta
kammala duk wasu shirye-shiryen da suka
wajaba a ce an yi, domin a tabbatar da an
gudanar da zabe sahihi mai inganci, adalci
kuma karbabbe a cikin kasa da ma duniya
baki daya.

No comments:

Post a Comment