Monday, November 19, 2018

[LABARAI] HUKUMAR ZABE TA KASA MAI ZAMAN KANTA TA TABBAR DA AMINU WAZIRI TAMBUWAL A MATSAYIN DAN TA KARAR GWAMNAN SOKOTO
Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta
tabbatar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a
matsayin dan takaran gwamnan jihar na zaben bana karkashin
jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga Jamilu dayamalam Gama

A cewar jaridar New Telegraph, kwamishanan hukumar INEC
kan ilimantar da msu zabe, Festus Okoye, ne ya tabbatar da
hakan.

A kwanakin baya da hukumar ta saki jerin sunayen yan takara,
an nemi sunan gwamna Aminu Waziri Tambuwal an rasa.

Okoye yace: “Jam’iyyar PDP tayi amfani da lokacin da hukumar
ta bada na daman iya sauya sunan dan takara wajen sanya
sunan Tambuwal.”

“Kamar yadda kuka sani, dokar zabe ta bayyana cewa kowani
dan takaran da jam’iyyar ta zaba na iy janye takararsa ta
hanyar rubutawa hukumar wasika wanda ya sanya hannu kuma
ya kai ofishin jam’iyyar da ta zabeshi.”

A jiya, jam’iyyar PDP ta yi wannan sauyin dan takaran
gwamnan jihar Sokoto. Sun sanya sunan Aminu Waziri
Tambuwal matsayin dan takara.”

No comments:

Post a Comment