Sunday, November 18, 2018

[LABARAI] Sanata Marafa, shugaban Karamar Hukumar Zurmi sun biya miliyan 11 aka saki tagwaye a Zamfara






Kamar yadda masu garkuwa suka bukaci a
biya su naira miliyan 15 kafin su saki wasu
tagwaye da suka sace a garin Dauran jihar
Zamfara, sanata Kabiru Marafa da shugaban
hukumar karamar hukumar Zurmi Awwal
Moriki ne suka biya naira miliyan 11 kafin
aka saki wadannan ‘yan mata.

Masu garkuwan sun bukaci sai an biya su
naira miliyan 15 kafin su saki wadannan
tagwaye da suka sace a daidai suna raba
katin auren su a garin Dauran.

Iyayen wadannan tagwaye mata sun yi ta
rokon al’umma da su taimaka koda karo
karo ne a ceci rayukan ya’yan su domin su
basu da irin wadannan kudade da masu
garkuwan suka nemi sai an biya su.

A kwanakin baya daya da ga cikin su ta aiko
da sakon murya tana cewa a gaban su an yi
ta yi wadanda ba su iya biyan kudin fansa
ba yankan rago.

A haka ne fa sanata Kabiru Marafa, cikin
tausayi ya aika wa iyayen wadanan mata
naira miliyan shida gudunmuwa domin a
hada da abin da aka samu wajen jama’a mai
taro mai sisi domin ceto rayukan wadannan
mata amare.

Shima shugaban karamar hukumar Zurmi
Awwal Moriki ya bada tasa gudunmuwar
naira miliyan 5.

Da Gusauloaded ta nemi ji daga
rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed
Shehu ya ce har yanzu ba su same cikakken
bayanai a kai ba. Sai dai kuma jaridar Daily
Nigerian ta wallafa a shafinta cewa ita har
ma tayi magana da wadannan tagwaye
bayan an sako su.

No comments:

Post a Comment