Lopetegui tsohon golan Barcelona da Real Madrid yana cikin matsi kan halin da Madrid din ke ciki a yanzu
Real Madrid ta kafa mummunan tarihi bayan da ta yi rashin nasara karo na hudu a wasa biyar, bayan da Levante ta doke ta a Bernabeu da ci 2-1.
Sakamakon ya kara jefa kociyanta Julen Lopetegui cikin matsi, inda kungiyar ta ci gaba da zama ta biyar a teburin La Liga, da bambancin maki uku a bayan ta daya Alaves mai maki 17 a wasa 9.
Sau biyu aka daga ragar Real Madrid a cikin minti 13, inda da farko a minti na 6 Morales ya fara ci, sannan kuma a minti na 13 Marti ya ci ta biyu da fanareti.
Yan wasan Real sun yi ta kai hare-hare masu kyau bal din na bugar karfen raga, a wasu lokutan kuma golan bakin Oier Olazabal ya kade ko ya kama.
A minti na 72 ne Marcelo ya kwararo wata bal ta yi wa mai tsaron ragar Levanten gaya-wa-jini-na-wuce ta kwana a ragarsa.
Kafin wasan na Asabar daraktan Real Madrid Emilio Butragueno ya nuna goyon bayansa ga kociya Lopetegui, to amma yadda suke fuskantar muhimmin wasa na gasar Zakarun Turai a gabansu, da kuma wasan hamayya da Barcelona, El Clasico a karshen mako na gaba, shugabannin kungiyar za su sha matsin lamba kan su hanzarta daukar mataki.
No comments:
Post a Comment