Wednesday, March 7, 2018

[LABARAI] HAIFAFFEN ZAMFARA YA SAMU NASARAR ZAMA SANATA A KASAR ITALIYAWani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin
kasar Najeriya ne da aka haifa a garin Gusau jihar
Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu
nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya
dake tarayyar turai a zaben da ya gudana.

Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami’in ‘yan kasar waje na jam’iyyar sa.

Manema labarai sun ruwaito cewa Mista Iwobi din ne ya sanar da samun nasarar ta sa a wani rubutun da yayi ya shelanta a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya godewa dukkan wadan da suka zabe sa.

A wani labarin kuma, Wata kungiyar matasan jam’iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar matasan Malam Sani Bello ya
fitar dauke da sa hannun sa a jiya Talata.

No comments:

Post a Comment