A kwanakin bayane dai kamfanin sadarwar na Airtel suka sanar da fitowar network dinsu mai
karfi da saurin browsing wato Airtel 4G LTE wanda wasu manyan garuruwa ke amfani da su
a halin da ake ciki.
A kokarin su na ganin sun rike kwastomomin su
masu amfani da wannan tsari a tattare dasu,
yasa kamfanin sanya wasu garabasoshi ga duk
masu amfani da wannan layi ba 4G LTE.
Kyautukan da kamfanin airtel ke bada wa akan
wannan sabon tsari na 4G LTE sune: 4GB data,
25% bonus (a yayin da ka sayi data ta N500
zuwa abinda yayi sama), sannan kuma zasu
siyar maka da tahunar network (Wi-Fi router)
da suke kira da Mi-Fi akan N10,000 kacal.
Kyautar 4GB Data din da suka baka zata yi
kwana 30 kana amfani da ita. Zaka ci gaba da
more 25% bonus din na tsawon wata 3 a duk
lokacin da ka sayi data ta N500 zuwa abinda
yayi sama. Za ka samu kyautar data da takai
4GB a MiFi router idan ka siyeta.
Ta yaya zan more wannan garabasa ?
Domin cin gajiyar wannan garabasa ta airtel 4G
LTE sai ka ziyarci ofishin airtel mafi kusa dakai,
sai ka nemi su yi maka swapping din layinka
daga 3G zuwa 4G. Za ka kuma iya ka siyi sabon
layi na 4G a sawwake.
Idan kayi daya daga cikin abubuwan da ke
sama, sai ka saka layin a wayarka sannan sai
ka maida network type dinka zuwa 4G.
Abin lura : Idan wayarka bata da tsarin 4G a
kanta to ba zaka iya more wannan garabasa ba
koda ka mallaki layin 4G din.
No comments:
Post a Comment