Thursday, February 15, 2018

[LABARAI] ANYI SALLAR JANA'IZAR SAMA DA MUTUN 35 DA BARAYI SUKA KASHE A MASARAUTAR ZURMIAnyi Jana'izar mutane sama da talatin da biyar da wasu 'yan bindiga
suka kashe a kauyen Birani dake karamar hukumar mulki ta Zurmi a
jahar Zamfara.

Da yamancin jiya Laraba 14//02//2018 ne wasu yan bindiga suka
kai mummunan hari a kauyen Birani dake cikin karamar hukumar
mulki ta Zurmi dake Jahar Zamfara, 'yan bindigar sun bude ma
motar 'yan kasuwa wuta motar tana dauke da mutanen kauyukan
birani, tungar fulani, mayasa da mashema, daga bisani kuma suka
cinna ma motar wuta wadda take dauke da dimbin mutane inda hakan
yayi sanadiyar hasarar rayuka da jikkita mutane da dama.

Sudai 'yan bindigar sun tare wata hanya ne dake fita garin na Birani
sukayi masu kwanton bauna inda suka tare wata motar 'yan kasuwa
kirar (kanta). 'yan kasuwar sun gama cin kasuwa ne kamar yanda
suka saba duk sati a hanyarsu ta zuwa garuruwansu sai 'yan bindigar
suka bude ma motar wuta tare da kone dukkan mutanen dake ciki
kuma suka cigaba da kashe mutane da sunkayi yunkurin kawo masu
dauki.

Jana'izar dai tasamu halartar Mai Martaba Sarkin Zamfaran Zurmi
Alhaji Atiku da Mai girma Shugaban Karamar hukumar Mulki ta
Zurmi Dr Auwal Bawa Moriki da dai sauran muhiman Mutane.

Allah yagafarta masu mukuma da muke da rayuwa Allah yayi muna
maganin abunda bamu iya yima kanmu.

Daga Saifullahi Yusuf Zurmi

No comments:

Post a Comment