Rikita rikita da ya balle tsakanin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuh
u da kuma shahararren dan fina finan Hausa, Adam A Zango, ya janyo
cece kuce tsakanin magoya bayansu, kamar yadda Gusauloaded.Ga ta gano.
Sai dai an samu wani matashin Kannywood, mai tasowa, Ali Artwork y
ana caccakar dukkaninsu jaruman, inda yace rainin hankali kawai suke
yi ma magoya bayansu masu kallon fina finansu.
Artwork ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace: “Duk
abunda kuka ga suna yi (Ali da Adamu) suna sane, kuma da gangan suk
e kirkirar hakan don su motsa jam’iyya, ka da a ce ai kwana biyu an m
anta da su. To ku sani, ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata.
Ali Nuhu, Artwork da Zango
“Idan baku manta ba a shekarun baya sun taba shirya irin wannan riki
cin, mu ka zo muka yi ta cece kuce a kai.
Amma daga karshe mai haka
n ta haifar sai suka maida mu ba mu san komai ba. dan haka kusan
duk wanda ya sa kansa sai ya yi da na sani.” Inji Artwork.
Jarumin cikin fushi bai tsaya nan ba, har sai da yace:
“Ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu, don a cikinsu babu wanda z
ai iya kashe min matsalar dubu 200,000. N zauna da kowa a cikinsu,
babu wanda bai more ni ba akan harka ta, ta editing. Amma babu wand
a na taba yi wa aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya ba ni, idan kuma
da akwai ya fito ya karyata ni.
“Sai dai kai ta bautar banza. sun fi so kullum ka yi ta ba su girma suna
zalintar ka to ku sani an yi walkiya mun ga kowa. Kyar Nake Kallonk
u. Ba ruwa na da rigimar wani, ni ma ta kaina nake. Idan kana yi da n
i, ina yi da kai, idan ba ka yi da ni, ni ma baruwa na da kai.”
Ali ya karkare babatunsa da sakon kai tsaye zuwa ga Ali Nuhu da A Za
ngo, inda yace: “Ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka ga dama ku sh
irya, ku ta dama ni ko a jikina, ko kuma mutum ya bar industiri din t
unda ba da ita aka haife shi ba, don haka mu za mu ciyar da harkar ga
ba insha Allah, tunda ku sai hassada da munafurci da gwara kan al'umm
a, ku je ku yi ta yi. Don haka ni na dogara da Allah, shi ne gatana ba
wani mutum ba.”
A kwanankin baya ma an samu kace nace tsakanin A Zango da Ali Nu
hu, inda A Zango da magoya bayan Ali Nuhu suka dinga musayar yawu
da mummunan kalamai, daga bisani ne manya suka shiga tsakani, har a
ka samu sulhu.
No comments:
Post a Comment