Tuesday, January 15, 2019

[LABARAI] MAHARA SUN KASHE MUTANE 26 A SOKOTO
Mahara sun kashe mutane 26 a garin Gandida ke Gundumar Karamar Hukumar Rabah ta Jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce an kai mummunan harin ne jiya Litinin da dare a kauyukan Warwana, Tabkin Kwasa da kuma Dutsi,
inda suka rika yin harbin kai mai uwa da
wabi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Murtala Mani ya
tabbatar da wannan hari. 

Mani ya shaida wa manema labarai cewa an kara kai jami’an tsaro a yankin domin
taimaka wa wadanda ke can a kamo maharan da suka yi kisan.

An ce dukkan su a kan Babura suka kai
harin.

Dama a cikin watan Yuli na shekarar da ta
gabata sai da aka kai wa garin hari aka
kashe mutane da yawa.

An kona kauyuka da dama a wancan hari
na watan Yuli da aka kai. 

Sarkin Goronyo Muhammadu Aliyu ya ce
muatane da ya yawa sun gudu sun bar
kauyukan.

Ya ce wadanda suka kai wannan harin ba
irin wadanda suka kai wancan harin na
baya ba ne. kuma ba irin masu zuwa suna
satar shanu ba ne.

Ya kara da cewa an kama akalla mutane 70 a cikin kauyuka 17 na yankin Goronyo a
cikin shekaru biyu. Kuma na biya diyyar da
ta kai naira miliyan 100.

Gwamna Aminu Tambuwal ya katse kamfen da ya ke yi a Goronyo, ya shaida wa mutane labarin kai harin, sannan kuma ya nemi a yi
addu’a.

No comments:

Post a Comment