Wednesday, January 16, 2019

[LABARAI] KALUBALE GUDA (5) DAKE GABAN SABON SUFETO JANAR NA YAN SANDA MOHAMMED ADAMU



Kalubale 5 Da Ke Gaban Sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu
 
Sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan
Najeriya, Sufeto Janar Mohammed Adamu, ya karbi ragamar shugabanci daga hannun Idris Ibrahim a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan kasar nan ke fuskantar babban kalubale.

Idan bai yi da gaske ba, zai kasance ya bi
layin wanda ya gada, ta yadda shi ma a
lokacin da zai kammala wa’adin sa zai
sauka ana korafi da shi da kuma yi masa
fatan Allah-raka-taki-gona kamar yadda
dimbin ‘yan Najeriya suka rika yi wa idris
wanda Adamu ya gada din.

Kalubale 5 da zai fara cin karo da su:

1- GARKUWA DA JAMA’A

Matsalar kashe-kashe da garkuwa da mutane a 

Arewa: Ko shakka babu idan aka dauki ‘yan watanni ba a ga ya tabuka komai ba, ba za a yi saurin yi masa tir ba. saboda ya zo a daidai lokacin da matsalar ta sakwarkwace har ma ta fi karfin ‘yan sanda.

A jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato
da Kaduna a yankin Birnin Gwari, abin ya fi
muni kwarai. Ya kamata Adamu ya gaggauta maye gurabun jami’an ‘yan sanda 250 wadanda Idris ya canja daga jihar Zamfara, amma har ya sauka bai maye gurbin su da ko da ‘yan kato-da-gora ba.

Zai yi kyau a gaggauta ware wata gidauniyar kudaden inganta rayuwar duk ‘yan sandan da za a tura domin ayyukan musamman a jihohin da garkuwa da jama’a ta yi kamari.

Ta haka ne za a kara musu kwarin gwiwa.

2- KAUCE WA BIYAN BUKATAR SIYASA

Sunan Sufeto Janar Idris ya baci wajen nuna siyasa karara a ayyukan ‘yan sandan
Najeriya suka rika gudanarwa a bisa umarni daga sama.

Wannan kuwa ya hada da garkame wadanda ba su shan inuwa daya da gwamnati, a gefe kuma ana kyale wasu masu laifi daga bangaren Gwamnati.

Matsawar ya tsoma kafar sa cikin sha’anin
siyasa, to tabbas kuwa zai taka kaya, kuma zai yi sartse.

3- ZABEN 2019

Da yawan wadanda suka rika fata da kuma addu’a kai har ma da wadanda suka rika tayar da jijiyar wuya cewa ba su yarda
Shugaba Buhari ya kara wa Idris wa’adi ko
na kwana daya ba, su na yi ne saboda ba su amince da shi ba a lokacin zabe.

Rawar da ‘yan sanda suka taka a zabuka
gwamna na jihohin Osun da Ekiti, ta zubar
da kimar Idris a matsayin sa na babban dan sanda na Najeriya. 

Babu yadda za a yi idris ya fita zargi a lokacin da ya tura ‘yan sanda 30,000 a zaben Ekiti, suka hana gwamnan lokacin, Ayo Fayose walwala, sannan kuma yawan su ya zama na wofi, domin ba su hana yin abin da aka ga dama a lokacin zaben ba.

Sannan kuma an kwashi wadannan dimbin
jami’ann tsaro ne zuwa Ekiti a lokacin da
ake tsanananin bukatar su a Zamfara, inda
fashi da garkuwa da kisan mutanen karkara ya yi kamarin gaske.

4- BAI WA ‘YAN ADAWA DAMA

Wani babban kalubalen da zai fuskanta shi
ne irin rashin adalcin da kwamishinonin
‘yan sandan jihohi ke nuna wa jam’iyyar
adawa a lokutan yakin neman zabe, wanda
a daidai lokacin ne aka nada wannan sabon Sufeto Janar, Adamu.

A jihohi kamar Kano, Kwara da Jigawa
jam’iyya mai mulki na cin karen ta babu
babbaka. A Kano APC na yawo da mukkan
makamai a tawagar kamfen na Gwamna
Ganduje, duk kuwa da cewa INE ta hana.
Amma babu ruwan jami’an ‘yan sanda da
hana su. Duk kuwa da kashe-kashen da akac rika yi a sanadinn haka.

5- RABA ‘YAN SANDA DA TUMASANCI

Cikin shekarar da ta gabata, Shugaban ‘Yan Sanda Idris wanda ya yi ritaya ya kafa
dokar janye ‘ayn sanda daga gidajen manya, wadanda akasarin su duk tsoffin gwamnoni ne, tsoffin ministoci da kuma wasu masu ci.

Bincike ya nuna al’umma na da karancin
jami’an tsaro, alhalinkuma dubban su na
can su na gadi da bilumbituwar raka wasu
manya da hamshakai karakaina.

Ya dace sabon shugaban ‘yan sanda ya
kwashe yawancin su daga wadannan
manya, a maida su cikin al’umma inda aka
fi bukatar su.

Matsawar Adamu ya tsaya a kan aikin sa, to nasara da kimar da zai fara samar wa kan sa ita ce kada ya bari ‘yan sanda su yi wa zabe katsalandan. 

Hakan zai sa a yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma ya kara wa yan sanda martaba.


No comments:

Post a Comment