Wednesday, January 16, 2019

[LABARAI] JEKADAN NIGERIA DAKE COTE D IVOIRE, IBRAHIM ISAH YA RASU

Jakadan Najeriya dake Cote d Ivoire, Ibrahim Isha, ya rasu

Labarin da ke shigowa yanzu na nuna cewa Allah ya yiwa jakadan Najeriya zuwa kasar Cote dbuwa, Ambasada, Ibrahim Isa, rasu a birnin Abidjan a ranan Talata, 16 ga watan Junairu, 2019 bayan doguwar jinya
da yayi.

Marigayi Ibrahim Isah ya fara aiki a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ne a shekarar 1983.

Ya yi aiki a ofishin jakandancin Najeriya a kasar Sierra Leone, jakadan Najeriya zuwa Amurka a birnin New York, a birnin Jiddah na kasar Saudiyya, da kuma ofishin jakadancin kasar Sin.

Ya kasance shugaban ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Ankara kasar Turkey kafin aka nadashi jakadan Najeriya zuwa kasar Cote d'Ivoire a shekarar 2018.

No comments:

Post a Comment