Sunday, November 11, 2018

[LABARAI] YAN TA'ADDA SUN SHIGA GARIN WANKE TA KARAMAR HUKUMAR GUSAU, SUN HARBI MUTUN DAYA, SUN TAFI DA MATA BIYU DA MAZA BIYU!








A Daren jiya wayewar safiyar Yau lahida 11-11-2018 da misalin
karfe 2:30 na dare barayi sunka shiga cikin garin wanke kilo
mita 15 daga Babban Birnin jahar Zamfara.

'Yan ta'addar sun harbi JUNAIDU WANKE Wanda Yanzu haka
yana assibiti. 

Sai kuma tafiya da matarsa karama da 'yarsa da
ake gab da daura mata aure tare da wani dansa. 

Haka zalika
'yan ta'addar sun shiga wani yi Nasarar yin garkuwa da wani
Dattijo ALHAJI BALA AJIYAN WANKE.

Garkuwa da mutane dan neman kudin fansa ya zama ruwan dare game duniya a jahar Zamfara. 

Domin da wahala a yini a kwana ba a saci wani Ko gungun mutane ba a jahar Zamfara.

Wanda Ko jiya an sace motar yan kasuwa kan hanyarsu ta shiga karamar hukumar Talata Mafara. 

Haka zalika Ko
makonni biyu anyi garkuwa da Wasu 'yan mata (Hasana da Husaina) biyu da su ka tafi yin Ziyarar 'yan uwansu a garin
Dauran a cikin karamar hukumar Zurmi.

Gwamnatin jahar Zamfara dai Ta kafa kwamiti na Musamman domin shago kan wannan matsalar tun daga yunkurin daukar 'yan Sakai da kuma ba da lada ta MILIYAN daya ga duk Wanda
ya nuna dan ta'adda da ke dauke da bindiga.

No comments:

Post a Comment